Pantami: ‘Yan Najeriya Sunyi Martani Kan Rage Kudin Data

 

Mutane da dama sun caccaki gwamnati a kan ikirarin ma’aikatar sadarwa ta rage 50% daga kudin data.

Ma’aikatar ta ce tayi ikirarin rage farashin data tun watan Janairun 2020 zuwa watan Nuwamba, hakan ya janyo cece-kuce.

Masu amfani da data, da kuma siyarwa daga jihohi daban-daban, duk sun musanta inda sukace basu ga wani canji ba.

Duk wani mai amfani da data a fadin kasar nan ya caccaki gwamnatin tarayya a kan ikirarin rage kudin data da 50%, Daily Trust ta wallafa.

Wata takarda, wacce ministan sadarwa, Dr Isa Ibrahim Pantami ya sanya hannu, yace an rage kudaden siyan data da 50% tun watan Janairun 2020, inda yace maimakon sayar da 1GB a N1000, ya koma N487.18.

Pantami ya ce ma’aikatar NCC ta samar wa wadanda suke sayar da data wannan rangwamen.

Kamar yadda takardar tazo bisa rahoton da NCC ta kaiwa mai girma ministan sadarwa, takardar da mataimakinsa na musamman, Mr Femi Adeluyi, ya fitar.

Sai dai mutane da dama sun musanta wannan ikirarin, inda suka ce basu lura da wani canji ba wurin siyan data.

Wani Deji Eluobomi, daya daga cikin masu siyan data a jihar Osun, ya musanta wannan ikirari, inda yace ba gaskiya bane don ko jiya da safe ya siya data 1GB a N1000.

Wani Eluobomi ya ce “Kila ba a fara bin tsarin ba har yanzu, don ko yau da safe N1000 na siya 1GB.”

Wani Muyiwa Ayinde Kareem daga Legas, ya musanta ragin 50% na kudin data, inda yace idan da gaske ne, shine mutum na farko da ya kamata ya sani don yana amfani da data kuma yana siyarwa.

Muktar Abdullahi daga Kano, ya ce bai ga wani ragi ba a batun siyar da data.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here