Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano na Bincike Kan Budurwar ‘da ta Rataye Kanta’

 

Rundunar ƴan sandan jihar Kano a arewacin Najeriya tana ci gaba da bincike kan abin da ya sa wata budurwa mai shekara 17 ta rataye kanta a ƙauyen Garin Dau da ke yankin karmar hukumar Warawa.

Mafi akasarin mazauna ƙauyen dai sun yi zargin cewar budurwar ta rataye kan nata ne bisa auren dole da iyayenta ke shirin yi mata.

Sai dai iyayen nata sun musanta wannan zargi inda suka ce ba ta kammala makarantar sakandare ba, balle a yi maganar aurar da ita.

Faruwar wannan lamari dai ya ya zowa mazauna yankin da mamakin sakamakon yadda da dama daga cikin mutanen kauyen ke bayyana budurwar da kyawawan ɗabi’u.

A yau ne aka shiga yini na biyu na rasuwar Safiya mai shekaru 17 da ke aji biyu a makarantar sakandare, wadda aka tarar da gawarta a rataye kuma ana zargin ita ta rataye kanta.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne mai magana da yawun rudunar ƴan sanda a Kano, ya shaida wa BBC cewa sun sami labarin faruwar lamarin, kuma suna bincike kan lamarin don gano shin budurwar ce ta rataye kan nata ko kuwa.

Wannan dai shi ne rahoton rataye kai na baya-bayan nan da aka samu a Kano, sabanin a watanin baya da suka gabata, biyo bayan kiraye-kiraye da wayar da kan al’umma da hukumomin jihar suka dauka.

A mafi akasarin lokuta ƙwararru a fannin sanin halayyar dan adam na alaƙanta ɗabi’ar mutum ya rataye kansa, sakamakon ciwon damuwa da yake fama da shi, ko wata larura da ta shafi kwakwalwa.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here