Rundunar ‘Yan Sanda Na Bukatar N24.8bn – IGP

IGP Mohammed Adamu ya ce rundunar na bukatar akalla biliyan 24.8 duk shekara domin zuba wa ababen hawansu mai.

Adamu ya bayyana hakan ne lokacin da yake kare kasafin kudin hukumar na 2021 a gaban kwamitin majalisar wakilai.

Ya ce an zaftare kasafin kudin da aka ware masu na 2021 zuwa biliyan 449.6 daga naira biliyan 469.4 Sufeto janar na yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu ya bayyana cewa rundunar za ta bukaci naira biliyan 24.8 domin zuba wa ababen hawanta mai a duk shekara.

Ya bayyana hakan ne a yayinda yake kare kasafinta na 2021 a gaban Kwamitin Ayyukan ’Yan Sanda na Majalisar Wakilai ta Tarayya.

Shugaban yan sandan ya bayyana hakan ne a yayin kare kasafin kudin 2021 a gaban kwamitin yan sanda na majalisar wakilai.

Ya bayyana cewa suna fuskantar tarnaki sakamakon rashin kebe masu isashen kaso a kasafin kudi. shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Adamu ya ce: “Babbar matsalar ita ce abinda aka ware mana ba zai ishe mu gudanar da ayyukan mu tsawon shekara guda ba. “Idan ka dauki misali, man fetur da ababen hawanmu ke sha a kulla-yaumin, motocinmu kan sha mai na kimanin naira biliyan 22.5 a cikin shekara kawai.

“Idan ka hada lissafin, a man fetur kawai an kusan karar da abinda aka ware mana, ba a ma zo ga bangaren gyare-gyare ba. Idan muna son kula da ababen hawanmu, muna bukatar akalla sama da naira biliyan takwas a shekara daya.”

Shugaban yan sandan ya ce a kudin da aka ware musu a kasafin 2021 na Naira biliyan 469.4 an zaftare shi zuwa Naira biliyan 449.6.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here