Rundunar ‘Yan Sanda Jahar Kano ta Cafke Wasu Matasa Masu Satar Mota

 

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Kano ta kama wasu matasa hudu da suka kware wajen satar mota.

Matasan hudu, mazauna unguwar Sheka, sun tsallaka gidan wani mutum Abba Adam tare sace motarsa bayan sun raunata matarsa .

Rundunar ‘yan sandan Nigeria reshen jahar Kano ta sanar da cewa ta gano tare da samun nasarar cafke wata tawagar barayin mota.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa ta bankado asirin tawagar barayin su hudu bayan kama daya daga cikinsu mai suna Al’amin Mohammed Bello, dan shekara 20, kamar yadda HumAngle ta rawaito.

A cewar Abdullahi Haruna Kiyawa, kakakin rundunar ‘yan sandan jahar Kano, jami’an rundunar Puff Adder a karkashin jagorancin CSP Musa Umar, sune suka kama matashin.

Kiyawa ya bayyana cewa an kama matashin ne yayin da yake kokarin sayar da wata motar sata.

Kakakin ya kara da cewa matashin ya bayyana sunayen sauran abokansa da suka hada Yusuf Lawan; mai shekaru 21, Abubakar Hassan; mai shekaru 28, da Yahaya Salisu; mai shekaru 28.

Kazalika, Kiyawa ya bayyana cewa matasan sun saci motar ne bayan sun balle gidan wani mutum mai suna Abba Adam.

Rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa Abba ya shigar da korafin cewa wasu batagari sun shiga gidansa sun raunata matarsa tare da sace motarsa.

Kiyawa ya sanar da cewa an garzaya da matar Abba zuwa asibiti yayin da su kuma barayin za’a gurfanar da su da zarar an kammala bincike.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here