‘Yan Sandan Kano Sun Ceto Budurwa Mai Shekara 20 Daga Hannun Masu Garkuwa
Jihar Kano – Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi holin wasu masu garkuwa da mutane guda biyu da aka yi nasarar cafkewa a Kaduna.
Mutanen biyu sun sace Hafsa, budurwa mai shekara 20 daga gidansu da ke Zarewa bayan an lakadawa mahaifin yarinyar, Alhaji Nuhu Zarewa dukan kawo wuka.
Jam’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa an yi nasarar ceto budurwar ba ko sisi
Miyagu sun shiga hannun yan sanda
Read Also:
Rundunar ‘yan sandan Kano ta kubutar da Hafsa da miyagu su ka sace zuwa Kaduna, inda likitoci su ka tabbatar da cewa ba a taba mutuncinta ba.
Haka kuma an yi nasarar ceto wani dattijo wanda miyagun su ka hada da budurwar a dajin da ke Makarfi da ke jihar Kaduna, sannan an damke mutanen da ake zargi.
Matashiya ta kubuta daga wajen miyagu
Mahaifin Hafsa, Nuhu Zarewa ya ce akalla miyagu 10 ne su ka shiga gidansa inda su ka yi masa dukan tsiya, tare da dauke ‘yarsa.
Alhaji Zarewa ya bayyana cewa bai biya ko sisi ba kafin rundunar ‘yan sanda ta kubutar da ‘yarsa ba, inda ya yi ta godiya da addu’ar alheri ga ‘yan sanda.
Daga cikin miyagun da aka kama akwai Yakubu Abubakar mai shekaru 40, wanda aikinsa shi ne tsaron mutanen da aka sato a kan N50,000.