‘Yan Sandan Jahar Katsina Sun Ceto Mutane 10 da AKai Garkuwa da su, Sun Kama ‘Yan Ta’adda 2

 

Rundunar ‘yan sandan jahar Katsina ta ce ta kama mutane 2 da ake zargin ‘yan ta’adda ne.

Har ila yau ta samu nasarar ceto mutane 10 da masu garkuwa da mutane su ka sace.

Kakakin rundunar, SP Gambo Isah ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Talata a Katsina.

Katsina – Rundunar ‘yan sandan jahar Katsina ta bayyana yadda ta kama mutane 2 da ake zargin ‘yan bindiga ne kuma ta ceto mutane 10 daga masu garkuwa da mutane.

Kamar yadda Daily Nigerian ta rawaito, kakakin rundunar, SP Gambo Isah, ya bayyana hakan a wata takarda da ya ba manema labarai ranar Talata a Katsina.

Isah ya bayyana yadda ‘yan sanda su ka yi musayar wuta da ‘yan bindiga

A cewar kakakin:

“A ranar 20 ga watan Satumban 2021, rundunar ta samu nasarar kama wani matashi mai shekaru 30 daga Sabon Garin Faguwa karkashin karamar hukumar Dutsinma wanda ya koma zama a daji.

“Shu’umin dan bindigan yana karkashin Sani Muhidinge ne, wanda yanzu haka ‘yan sanda suke nema ido ruwa a jallo.

“Sannan sun kama wani takadarin dan bindiga mai shekaru 22 dan Mai Gezoji, Tashar Mai Alawa dake karkashin karamar hukumar Danmusa.

“Tushen lamarin shine yadda ranar 15 ga watan Satumban 2021 ‘yan bindiga suka shiga kauyen Kitibawa dake karamar hukumar Dutsinma da kafa su na harbe-harbe.

“Sakamakon harbin sun hallaka ‘yan kauyen guda 2, sun banka wa shaguna wuta sannan suka sace mata 18 da jarirai 7.

“Bayan samun wannan labarin ne kwamandan ‘yan sanda na Dustinna, ACP Aminu Umar, ya jagoranci rundunar sa suka dakatar da ‘yan bindigan su ka fara musayar wuta.

“Sakamakon jajircewar ‘yan sandan da jarumtar su ya sa ‘yan bindigan su ka ji aman wuta su ka tsere daji da raunuka da dama.

“Bayan mayar da harin ne ‘yan sanda su ka ceto mata 2, tumaki 60, shanu 34 da jaki daya.”

Kamar yadda Isah ya shaida, binciken sirri da su ka gudanar ya sa a ranar 20 ga watan Satumba su ka kamo wani mutum mai shekaru 45 dan Tashar Mai Alawa dake karamar hukumar Danmusa da ake zargin ya na bai wa ‘yan bindiga labaran sirri kamar yadda Daily Nigerian ta rawaito.

Sannan sun kara kama wani mutum mai shekaru 34 wanda ma’aikacin asibiti ne, inda yake yi wa ‘yan bindiga aiki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here