‘Yan Sanda Sun Ceto Mutane 20 da ‘Yan Bindiga Suka yi Garkuwa da su a Jahar Neja
‘Yan sandan Neja sun ceto mutum 20 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su sakamakon samamen da suka kai kan sansanin ‘yan fashin daji a jihar da ke tsakiyar Najeriya.
Kakakin rundunar a Neja, DSP Wasiu A. Abiodun, ya faɗa cikin wata sanarwa ranar Lahadi cewa dakarunsu sun kai samamen ne a yankin Anaba da ke Ƙaramar Hukumar Magama.
Read Also:
Bayan fafatawa gami da harbe-harbe tare da ‘yan bindigar, dakaru sun yi nasarar kashe ‘yan fashin tare da ƙwato shanun da suka sata.
“Ƙarin dakarun da aka tura ciki har da sojoji da ‘yan banga sun fara fafatawa da ‘yan bindigar a kan hanyar shanu da Ibeto kusan tsawon awa biyu a lokacin da maharan ke ƙoƙarin guduwa,” in ji shi.
Daga cikin makaman da aka ƙwace daga hannunsu sun haɗa da bindigar AK-47 ɗaya da ƙunshin harsasai 30 da wayar salula bakwai da babur ɗaya, a cewar DSP Abiodun.