ENDSARS: ‘Yan Sanda Jahar Legas Sun Mamaye Lekki Toll Gate Don Dakatar da Zanga-Zangar
‘Yan sanda sun mamaye Lekki toll gate da ke Legas ana jajiberin ranar da masu zanga-zanga za su fito.
Runduna ta musamman ta hukumar ‘yan sandan jahar Legas ne suka tabbatar da cewa jami’an ‘yan sandan sun mamye wurin.
Dama jama’a sun yi niyyar fara zanga-zangar ne bayan kotu ta amince da bukatar kara bude toll plaza.
‘Yan sandan jahar Legas sun tsaya tsayin daka wurin dakatar da zanga-zangar End SARS wacce matasa suka shirya farawa a ranar Asabar a Lekki toll gate.
Read Also:
Runduna ta musamman ta ‘yan sandan jihar Legas ne suka tabbatar da dakatarwar, The Nation ta ruwaito.
“CSP Yinka Egbeyemi wanda yanzu haka ya jagoranci ‘yan sanda domin tsaron Lekki Toll Gate (Admiralty Plaza) Obalende, Ikoyi, Jakande Roundabout, da wasu bangarori na Eti Osa,” kamar yadda RRS suka wallafa a shafinsa na Twitter ranar Juma’a da daddare.
Hukumar ‘yan sanda tana iyakar kokarin ganin ta kara baiwa jami’anta na bangarorin kwarin guiwa.
Dama an shirya yin zanga-zangar ne bayan wasu mutane 9 sun bukaci amincewar kotu don a kara bude toll plaza.
Shugaban, Alkali Doris Okuwobi da wasu mutane 4 su ne suka bukaci LCC ta kara bude wurin.