Oyo: Rundunar ‘Yan Sanda ta Damke Fulani 47 Dauke da Makamai
Rundunar ‘yan sanda sun kame wasu Fulani da ake zargi masu garkuwa da mutane ne.
An kama Fulanin da gungun muggan makamai a wani yankin jahar Oyo.
‘Yan sanda sun bayyana cewa Fulanin na kan hanyarsu ta zuwa daukar fansa ne sadda a ka kame su.
Rundunar ‘yan sanda reshen jahar Oyo ta tabbatar da kame wasu Fulani 47 dauke da makamai a yankin Igangan da ke karamar hukumar Ibarapa ta Arewa a jahar, The Sun ta ruwaito.
Jami’an tsaro na hadin guiwa na rundunar yaki da masu aikata laifuka ta jihar karkashin jagorancin sojoji ne suka damke mutanen dauke da makamai a kogin Ofiki da ke kan titin Tapa-Igangan.
An kama su ne bayan wasu sa’o’i bayan da Hukumar Tsaro ta Jihar Oyo, wanda aka fi sani da Amotekun Corps, ta kai samame a maboyar wasu da ake zargin masu satar mutane ne da safiyar Asabar.
An ba da rahoton cewa an kashe ‘yan fashin guda uku a ranar Asabar, tare da wani memba na Vigilante Group of Nigeria shi ma ya ji rauni yayin samamen.
Fulanin da ake zargin 47 ne dauke da makamai, a cewar wata majiya, an kai su ne a cikin motocin bas uku.
An bayar da rahoton cewa hukumar tsaron ta kwato daga wadanda ake zargin bindigogin Dane 47, baka, kibiyoyi, wukake, adduna, da kuma wasu manyan bindigogi wadanda aka boye su a cikin motocin bas din.
Read Also:
An bayyana cewa mutanen 47 dauke da makamai suna kan hanyarsu ta zuwa daukar fansa ne zuwa Ibarapaland biyo bayan mutuwar mutane ukun da ake zargin ‘yan fashi ne.
Ana zarginsu da addabar yankin ta hanyar kashe-kashe da sace-sacen mutane da ke kara tabarbarewar tsaro a jahar ta kudu maso yamma.
Mai magana da yawun ‘yan sanda Olugbenga Fadeyi, wani Babban Sufeton ‘yan sanda (CSP), ya ce yayin da yake tabbatar da kamun cewa an mayar da Fulanin da aka kama zuwa SCID (Sashin binciken manyan laifuka na Jaha) na Iyaganku, Ibadan don bincike mai zurfi.
“Duk da cewa an yi zargin fulanin sun yi ikirarin cewa suna bin sahun wasu masu satar mutane wadanda ke shirin karbar kudin fansa daga dangin wanda aka sace, ana ci gaba da bincike kan kamun…”
Kodinetan OPC a shiyyar Ibarapa, Olanrewaju Ogedengbe, ya ce: “An kama mutane arba’in da bakwai daga cikin su a Kogin Ofiki.
“An kama su da bindigogin Dane kuma bayan an bincika motocin bas ɗin su; an kuma gano manyan bindigogi, baka, kibiyoyi, layu, katafila, da harsasai. Wadanda aka kama sun ce an kawo su ne daga Ilorin, Iseyin da sauran wurare.”
Kwamandan rundunar Amotekun a jihar, Col Olayinka Olayanju (mai ritaya), ya ce aikin share fage da aka gudanar a ranar Asabar ya samu cikakken goyon baya daga shugabannin Fulani, wadanda ke zaune a yankunan.
Ya kara da cewa wasu mambobin kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria ( MACBAN), sun kasance ɓangare na ayyukan.