Hana su Hakkokkinsu: Jami’an ‘Yan Sandan Jahar Zamfara Sun Nuna Fushin Su Akan Gwamna Matawalle

Bello Matawalle ya gamu da fushin ‘yan sanda bayan ‘yan bindiga sun yi ta’adi ‘Yan sanda sun tasa.

Gwamna a gaba da ya zo duba gawar jami’an da aka kashe Jami’an tsaron na zargin Gwamna da hana su hakkokinsu, da rashin kula da su.

‘Yan Sanda sun yi fushi da gwamnan jahar Zamfara Ganin yadda sha’anin tsaro ke tabarbare wa a jahar Zamfara,

wasu fusatattun jami’an ‘yan sanda sun huce takaicinsu a kan mai girma gwamna.

Jaridar PR Nigeria ta fitar da rahoto cewa wasu daga cikin rundunar ‘yan sanda da ke Zamfara, su na fushi da gwamna Bello Mohammed Matawalle.

Jami’an tsaron na zargin Bello Mohammed Matawalle da laifin wasa da hakkokinsu, watsi da su, da kuma kin damu wa da mugun halin da suke ciki.

Wasu ‘yan sanda sun yi wa gwamnan ihu yayin da ya ziyarci asibitin kwararru na Bello Mohammed Matawalle da ke garin Gusau, Zamfara.

Gwamnan ya zo ne musamman domin ganin gawar wasu jami’an ‘yan sanda 13 da ake zargin ‘yan bindiga sun hallaka a Kurar Mota, garin Bungudu. Wani wanda abin ya faru a gabansa, yace gwamnan ya ci karo da fusatattun jami’an ‘yan sanda daga cikin wadanda suka yi rai a harin ‘yan bindigan.

‘Yan sandan sun koka kan cewa sun bukaci a karo masu jami’an tsaro a fagen fama, amma babu wani wanda ya bi ta kansu, baya ga karancin harsashi.

Wadannan dakaru na MOPOL sun yi ta surfafa wa gwamna munanan kalamai marasa dadi, har ta ai wani daga cikinsu ya nemi ya taba Bello Matawalle.

Daily Post ta ce jami’an tsaron sun zargi gwamnan da hana su alawus na kusan shekara guda, duk da cewa su na jeji wajen fada da miyagun ‘yan bindiga.

Sai dai a doka da tsarin mulkin Najeriya, ba gwamna ba ne yake da iko da sha’anin ‘yan sanda.

Bello Mohammed Matawalle ya yi alkawarin zai share wa’yan sandan hawayensu, zai kawo karshen rashin biyan alawus da sauran korafin da su ke yi.

Dazu kun ji cewa wani rahoto da aka fitar, ya nuna a watan da ya gabata, duk rana ta Allah, sai miyagu sun hallaka akalla mutum 34 a cikin jahohin Najeriya.

Boko Haram, ‘Yan bindiga, da sojojin IPOB sun yi ta’adi a kananan hukumomi 127 a Jahohi 34.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here