Kwana 1 da Haihuwa: Rundunar ‘Yan Sandan Jahar Kano ta Gano Jaririn da Aka Sace

‘Yan uwa da dangin wasu yara a jahar Kano na ci gaba da bayyana irin halin da suka shiga, bayan sace daya daga cikin ‘yan biyun da wata ‘yar uwarsu ta haifa da ake zargin wasu ma’aurata sun yi, kwana daya da haihuwarsu.

Rundunar ‘yan sandan jahar Kano ta tabbar wa BBC sace jaririn a hannun kanwar mahaifiyarsa da ke jinyar mai jegon sanda bacci ya dauke ta, a asibitin Nasarawa a jahar.

Rundunar ‘yan sandan ta ce an gano inda yaron yake ne bayan samun labarin wata mata da aka ce ta haifi da namiji, ba tare da ta sami ciki ba.

Malama Bara’atu Muhammad kanwar matar da aka sace wa daya daga cikin ‘yan biyun a asibitin Nasarawa dake Kano ta bayyana wa BBC cewa lamarin ya matukar girgiza ta.

Shima mahaifin jaririn Rabi’u Muhammad, ya bayyana farin cikinsa dangane da gano dan nasa.

Yanzu dai ma’auratan da ake zargi da sace jaririn na hannun rundunar yan sandan jahar Kano inda ake ci gaba da gudanar da bincike.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here