‘Yan Sandan Jihar Kaduna Sun Gayyaci Mutane 5 Kan Mutumin da Aka Rufe Tsirara na Tsawon Shekaru 20

 

Yan sanda a Kaduna sun gayyaci mutane biyar domin taimaka musu da bincike kan mutumin da aka gano an rufe a daki.

A ranar Laraba ne rundunar yan sandan suka ceto mutumin a wani gida da ke Bayajida cikin daki da ake ce an rufe shi kimanin shekaru 20.

Yan sandan sun ce binciken da suka fara ya nuna mutumin yana da mata da yara amma a halin yanzu ba a san inda suka tafi ba.

Kaduna – Rundunar yan sanda a Kaduna ta gayyaci wasu mutum biyar don taimaka mata a binciken da ta ke yi kan rufe wani mutum dan shekara 67 a na tsawon shekaru 20 a Kaduna.

Kakakin yan sanda DSP Muhammad Jalige, ya bayyana hakan a ranar Laraba, Daily Trust ta rahoto.

An ceto mutumin, Mr Ibrahim Ado, ne a wani gida da aka rufe shi a Bayajiadda/Ibrahim Taiwo Road, karamar hukumar Kaduna ta Arewa a ranar Laraba.

Jalige ya fada wa manema labarai cewa ma’aikatan duba gari da ke aiki a Bayajiadda by Ibrahim Taiwo Road a Kaduna ne suka kai rahoto.

A cewarsa, bayan samun rahoton, kwamishinan yan sandan Kaduna, Yekini Ayoku, ya tura mutane zuwa wurin suka fito da mutumin.

Ya ce kwamishinan ya bada umurnin a bincika dalilin da yasa aka tsare mutumin tsawon lokaci. Ya ce an rufe mutumin kusan shekaru 20, a can ciki ya ke cin abinci, fitsari da komai.

Ya ce:

“Mun tafi wurin, mun tarar da shi ba tufafi, mun bashi kaya ya saka kuma muka fito da shi muka kai shi asibiti a duba shi.”

Jalige ya kara da cewa kwamishinan yan sandan na Kaduna ya kuma bada umurnin yin sahihin bincike don gano ainihin dalilin da yasa aka yi wa dattijon irin wannan rashin tausayin.

Ya ce DPO na ofishin yan sanda na Magajin Gari ya fara bincike kuma za a gano ainihin abin da ya faru.

Mun samu mutum 5 da ke taimaka mana – Jalige

Ya ce sun samu wasu mutane biyar a unguwar da ke taimaka musu a binciken da suke yi.

Jalige ya ce:

“An fahimtar da mu cewa mutumin yana da yara da mata amma ba a san inda suka tafi ba, muna kyautata zaton mutanen da muka tarar a gidan da makwabta za su taimaka mana gano ainihin abin da ya faru.”

“Za mu yi aiki tare da likitoci domin samun rahoto kan lafiyarsa. Abin da ya fi muhimmanci shine a duba lafiyarsa da bashi kulawa, kuma mun yi nasarar yin hakan.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here