‘Yan Sanda Sun Harbe ‘Yan Fashi a Adamawa
‘Yan sanda a jahar Adamawa tare da hadin kan ‘yan banga da mafarauta sun samu nasarar kashe ‘yan fashi.
Sun kuma samu nasarar kame daya daga cikin ‘yan ta’addan a yayin farmakin
‘Yan sandan sun bayyana cewa suna kan bincike kan yadda za agurfanar da dan fashin
Wani farmaki da wasu jami’an ‘yan sanda, ‘yan banga da mafarauta a jihar Adamawa suka kai wa mambobin kungiyar ‘yan fashi ya yi sanadiyyar kashe biyu daga cikin ‘yan fashin tare da kame daya.
Sauran mambobin kungiyar sun tsere bayan an ci karfinsu a farmakin, wanda ya faru da sanyin safiyar Litinin a kusa da karshen Numan na Babbar Hanyar Numan zuwa Jalingo, The Nation ta ruwaito.
DSP Suleiman Nguroje a jahar ta Adamawa, ya ce a cikin wata sanarwa da safiyar Litinin din da ta gabata an fara gudanar da aikin tsaro cikin nasara bisa umarnin kwamishinan ‘yan sanda, CP Aliyu Adamu.
Read Also:
“Bayan wani mutumin kirki” ya ba da rahoton cewa wadanda ake zargi da fashi suna barna.
Ya kara da cewa aikin tsaro, wanda DPO mai kula da Numan Division ya jagoranta, ya sami nasarar saboda DPO ya yi sauri wajen tattara mutanensa da mambobin kungiyar sa-kai da kungiyar mafarauta.
A cewarsa, an kwato bindigogin, da wukake masu kaifi, adduna da layu daga wadanda ake zargin a daidai lokacin da aka damke daya daga cikinsu, Ashidu Balari, mazaunin Lafiya a karamar hukumar Lamurde ta jihar Adamawa tare da raunin da ya samu daga harbe-harben.
“Wanda ake zargin wanda yanzu haka yake karbar kulawar asibiti ana bincikar shi dangane da makircin laifuka da fashi da makami.
“A halin yanzu, Rundunar ‘yan sanda ta yaba wa jami’an ‘yan sanda na Numan Division saboda matakin da suka dauka na gaggawa wanda ya haifar da nasarorin da aka samu.”
Karshe hukumar ‘yan sanda ta bayyana cewa “Za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zaran an kammala bincike,” in ji Nguroje.