Rundunar ƴansandar Rivers ta Janye Jami’anta Daga Sakatariyar ƙananan Hukumomin Jihar
Rundunar ƴan sandar jihar Rivers ta janye jami’anta daga dukkan sakatariyar ƙananan hukumomi 23 da ke jihar, hakan na zuwa ne bayan kammala zaɓen ƙananan hukumomin tare da rantsar da wadanda suka yi nasara.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Rundunar ƴansandar, Grace Iringe-Koko , ta fitar da safiyar yau Litinin ta tabbatar da hakan.
Ta ce kwamishinan ƴansanda na jihar ya bayar da umarnin ne ƙarƙashin umarnin Sifeto Janar, Kayode Egbetokun, wanda ya umarci a janye jami’an da ke samar da tsaro a dukkan hedikwatar ƙananan hukumomin jihar nan take.
Read Also:
Jam’iyar APP ce ta samu nasarar lashe zaɓen ƙananan hukumomi 22 a cikin 23, yayin da jam’iyar AA ta samu nasarar lashe zaɓen ƙaramar hukumar, Etche.
Jami’an ƴansandan dai sun ƙarɓe iko da hedikwatar ƙananan hukumomin jihar Rivers a watan Yuni sakamakon rashin fahimta da ta shiga tsakanin Kantomomi masu goyon bayan gwamnan jihar mai ci Siminalayi Fubara da kuma tsoffin shugabannin ƙananan hukumomi na gwamnatin da ta gabata da ke goyon bayan tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja, Nyesom Wike.
Gwamna Siminalayi Fubara na takun saƙa da tsohon uban gidansa, ministan Abuja, Nyesom Wike, inda kowanensu ke son samun rinjaye a siyasance a jihar.
Rikicin ya sanya yaran gwamna Fubara barin jam’iyar PDP, inda suka yi takara a jam’iyar APP.