‘Yan Sanda Sun Kama Bata-Gari a Jahar Kaduna
Wata rundunar ‘yan sanda a jahar Kaduna sun samu nasarar cafke wasu bata-gari a jahar.
Sun kame mutanen biyu ne dumu-dumu da zargin laifin satar motoci a cikin jahar Kaduna.
Sun kuma samu nasarar kwato motoci daga hannun barayin, yayin da suka bayyana lambobin motocin Rundunar ‘yan sanda a jahar Kaduna ta samu nasarar cafke wasu masu satar mota su biyu a yankin Nassarawa na babbar hanyar Nnamdi Azikiwe da aka fi sani da Western bypass, Daily Trust ta ruwaito.
Read Also:
‘Yan sanda sun kuma gano karamar mota kirar Toyota Camry dauke da lambar rajista ABC 590 DX da Toyota Corolla mai launin toka dauke da lambar rajista KTN 304 AG, daga wadanda ake zargin.
A cewar kakakin rundunar, ASP Mohammed Jalige, an kama wadanda ake zargin ne a ranar 2 ga watan Fabrairun 2021, daga jami’an rundunar da ke aiki a sashen Kakuri yayin da suke sintiri a kan babbar hanyar Nnamdi Azikiwe da ke kan hanyar Nassarawa Bridge a Kaduna.
Ya bayyana sunayen wadanda ake zargin da Abubakar Abdullahi na Hayin Danmani da Gambo Musa na yankin Rigasa, duk a karamar hukumar Igabi ta jahar.