‘Yan Sanda Sun Kama Wasu Batagari da Makamai

Yan sanda sun kai samame maboyar masu aikata miyagu ayyuka a jihar Lagas.

A cikin haka, sun yi nasarar kama mutane 720 da makamai a fadin sassa 14 na jihar.

Hakan ya faru ne a ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamba Rundunar yan sanda a jihar Lagas a ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamba, ta bayyana cewa ta kama mutane 720 mabuya daban-daban a jihar duk a cikin kokarin da ake na kakkabe laifuka.

Olumuyiwa Adejobi, kakakin yan sandan jihar, a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa rundunar ta kai samamen ne a ranar Lahadi sannan ta kama masu laifin a yankuna 14. An kuma samo makamai, layoyi, da miyagun kwayoyi.

Mista Adejobi ya ce rundunar yan sandan jihar sun sake kaddamar da dabarunsu na yaki da masu laifi domin kakkabe miyagun laifuka a fadin jihar.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa wasu daga cikin kayayyakin da aka karbo ana zaton an sato su ne a lokacin hare-haren da aka kai na fasa shaguna a yayin zanga-zangar EndSars.

Tuni dai kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hakeem Odumosu ya bayar da umarnin fara da bincike kan mutanen da aka kama domin gurfanar da su a gaban kotu, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

Har ila yau, ya nemi wadanda aka yi wa sata a yayin zanga-zangar EndSars da su zo su duba kayayyakinsu da kuma shaidar cewa sune mamallakan kayan.

Ya kuma yaba wa ‘yan sandan jihar bisa jajircewarsu wurin wannan samamen da suka kai.

Ya kuma bukaci jami’an tsaron da su kasance cikin ko ta kwana domin aiwatar da irin wannan samamen a nan gaba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here