‘Yan Sanda Sunyi Nasarar Kama Wani ‘Dan Damfara

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kano sun kama wani matashi, Gambo Yakubu, bisa zarginsa da sojan gona da damfara.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce mutumin ya damfari mutane 15 sama da Naira dubu dari bakwai.

An gano cewa matashin ya dauki budurwarsa tare da tafiya wani Otal a Sabon Gari inda suka kashe kudin jama’ar da ya damfara.

Hukumar yan sandan Nigeria reshen jihar Kano ta tabbatar da kame wani mutum dan shekara 30 bisa laifin damfarar mutane sama da Naira 700,000.

Mutumin, mai suna Gambo Yakubu, an kama shi ne bayan ya damfari mutane kudi sama da N700,000 ta hanyar amfani da sunan babban kaftin din kungiyar kafa ta Najeriya, super Eagles, wato Ahmad Musa.

Mutumin na fakewa da sunan zai taimakawa mutane domin su samu damar kwantiragi da kungiyoyin ƙwallon ƙafa dake Turai, inda ya ke neman su kawo kuɗi domin samun wannan damar.

Biyo bayan kama shi ɗin ne, sai aka same shi da takardu dake ɗauke da sunan shahararren ɗan ƙwallon ƙafar nan Ahmad Musa, wanda ya ke amfani da su don samun biyan buƙatar sa.

Jaridar Premium Times ta ce, “Ana zaton ya damfari mutane sama da 15 ta wannan hanyar wanda adadin kuɗin su ya haura N700,000 daga bisani kuma ya kashewa budurwarsa kuɗaɗen a wani hotel da suke zama cikin Sabon Garin Kano.”

A ta bakin wanda ake zargi, Yakubu ya ce, “Ya na sayar da fom kan kudi N5000 matasa da suke tsananin buƙatar buga ƙwallo a ƙasashen waje.”

DSP Abdullahi Haruna, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ya tabbatar da kama matashin wanda shima ya taɓa bugawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya Super Eagles.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here