Sifeto Janar na ‘Yan Sanda ya Shigar da Karar Wani Babban ‘Dan Jarida

IGP Mohammed Adamu, babban sifeton rundunar ‘yan sanda, ya shigar da karar mai gidan jaridar SaharaReporter, Omoyele Sowore.

Adamu ya garzaya kotu ne tare da neman Sowore, tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2019, ya bashi hakuri a kan kazafin da ya yi masa.

Kotu ta tsayar da ranar 26 ga watan Janairun sabuwar shekara domin fara sauraron karar da IGP Adamu ya shigar .

Babbar kotun tarayya dake Abuja ta amince da karɓar karar da shugaban hukumar yan sanda, IGP Mohammed Adamu, ya shigar gabanta akan ɗan gwagwarmayar nan kuma mai gidan jaridar yanar gizo Sahara Reporters, Omoyele Sowore.

Mai shari’a, Binta Mohammed, ce ta amince da sauraron ƙarar wacce lauyan mai kara, Alex Izinyon, ya shigar inda suke neman kotu da ta ci tarar Sowore Naira biliyan 10 bisa rahoton karya da suke zarginsa da bugawa a jaridarsa, kamar yadda Daily Nigerian.

auya Izinyon, ya buƙaci kotu da ta “lamincewa mai ƙara, IGP Adamu, shigar da korafi kan wanda ake zargi, watau Sowore, wanda yake zaune a No. 1, Mosafejo Street, Kiribo, ƙaramar hukumar Ese-Odo, jihar Ondo.”

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN, ya rawaito inda IGP Adamu ya bayyana rahoton da shi Sowore ya buga a ranar 3 ga watan Agusta cewa yarfe ne da ƙage.

Sowore dai ya buga labarin cewa, Shugaban yan sanda na ƙasa ya tattara wasu makudan kudade ta barauniyar hanya don gina wata makarantar horar da yan sanda a jihar Nasarawa.

IGP Adamu, ta bakin lauyansa, Izinyon, ya yi barazanar sai Sowore da kafar yaɗa labaransa sun ba shi biliyan goma bisa wannan maganar ko kuma su wallafa sakon neman afuwar sa a cikin kwana bakwai.

Mai shari’a Binta ta daga sauraron karar zuwa ranar 26 ga watan Janairun sabuwar shekarar 2021.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here