‘Yan Sandan Najeriya Sun Kama Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane a Hanyar Abuja-Kaduna
Yan sanda a Najeriya sun ce sun kama wani da ake zargin kasurgumin mai garkuwa da mutane ne tare da wasu mutum 29 na daban,
‘Yan sandan sun ce mutane suna da hannu a yawancin garkuwar da ake yi da mutane da fashi da makami wadanda suka fi mayar da hankali a kan hanyar Abuja-Kaduna har da ma cikin Kaduna.
Read Also:
Mutumin mai shekara 36 ya amsa cewa shi yake jagorantar kungiyar, cikin wata sanarwa da ‘yan sanda suka fitar a yammacin Alhamis.
Hanyar Abuja-Kaduna na daya daga cikin hanyoyi masu matukar hadari a Najeriya yayin da masu garkuwa da mutane ke yi wa matafiya kwantan bauna a hanyar.
Sau da yawa ke kama harbin kan mai uwa da wabi domin tursasa musu tsayawa a hanya.
An kashe matafiya da yawa a hatsaniya wadanda kuma suka tsira sai a yi garkuwa da su kuma ana sakinsu ne bayan sun biya kudaden fansa.
Wannan dalili ya tilastawa mutane da dama daina bin hanyar suka koma jirgin kasa – wanda suke ganin hakan a matsayin wani tudun mun tsira daga bin hanyar.