‘Yan Sanda Ghana Sun Kama Sanannen ‘Dan Kwallon Kafa, Fire Man da Kawunan Mutane 3
‘Yan sandan kasar Ghana sun damki wani sanannen dan kwallo, Richard Gyamfi wanda aka fi sani da Fire Man da kawunan mutane 3 a firjinsa.
Bayan bayyanar lamarin ne, wani mutum da ya rasa dan sa yace dan kwallon ya yaudari dan sa mai shekaru 13 inda ya kai shi dakin shi ya kashe shi.
Kamar yadda abokansa da suka je filin kwallon tare suka tabbatar, sun gan shi tare da Fire Man, bayan ya musa ne aka balle kofarsa aka ga gawar.
Ghana – Hukumar ‘yan sandan kasar Ghana sun kama wani dan kwallon kafa, Richard Gyamfi wanda aka fi sani da Fire Man da kawun mutane 3 a firjin sa a wuraren Sunyami, shafin Linda Ikjei ya rawaito.
Gidan rediyon Sky FM dake Sunyami sun tabbatar da aukuwar lamarin inda suka ce mahaifin daya daga cikin mamatan, Mr Thomas Aygei ya bayyana yadda wanda ake zargin ya yaudari dansa, Louis Agyemang Junior mai shekaru 13, a filin kwallo da ke Sunyami Abesum har dakinsa inda ya hallakasa.
Read Also:
Yaro mai shekaru 13 ya bar gida, bai koma ba
Da yake tagwaye ne yaron da dan uwansa, mamacin ya bar gida zai tafi filin kwallon. Daya daga cikin abokan mamacin, mai suna Tweneboa sun tabbatar wa da mahaifin cewa sun gan shi tare da Fire Man.
An fara zargin Gyamfi tun bayan ya musanta ganin yaron bayan an fuskance shi da maganar, shafin Linda Ikeji ya wallafa.
An balle kofar dakin Gyamfi domin bincike
Bayan iyayen yaron sun kai wa dan kwallon ziyara gidansa sun tarar dashi a kulle. Bayan an balle kofar ne aka ga gawar Louis Agyemang Junior a kwance an cire masa kai.
Wanda ake zargin ya sha gwale-gwale kafin aka mika shi ga ofishin ‘yan sanda dake Sunyami Abesim. Bayan ‘yan sanda sun duka dakin sa, sun ga gawa a cikin buhu sannan sun ga kawunan mutane uku ciki har da na Louis Agyemang.
‘Yan sandan Abesim sun mika shi zuwa ofishin ‘yan sanda na yankin Borno don cigaba da bincike.
Yanzu haka kawunan guda uku ciki har na Louis Agyemang Junior suna ma’adanar gawa ta Best Care dake kudancin Sunyani.