‘Yan Sanda Sun Kama Mai Kula da Lafiyar ‘Yan Bindiga a Katsina

 

Yan sanda sun damke mai kula da lafiyan tsagerun yan bindiga a Katsina.

Matashin ya bayyana cewa shi ke sayar musu da maguna kuma yake musu jinya.

Ya yi nadamar abinda yayi kuma idan aka yafe masa ba zai sake ba.

Katsina – Wani ma’aikacin lafiya a jahar Katsina, Murtala Umar, ya bayyana yadda ya kasance mai kula da yan bindiga yayinda suka samu raunuka duk da cewa ya san yan ta’adda ne.

A ranar Litinin, hukumar yan sanda a jahar Katsina ta gabatar da shi gaban manema labarai a hedkwatar hukumar, rahoton Premium Times.

Malamin jinyan mai suna Murtala ya bayyanawa manema labarai cewa dole ce ta sa shi yake aiki da su.

Murtala na da shagon sayar da magunguna a Tashar Yar Alewa, dake karamar hukumar Danmusa.

Al’ummar garin ne suka sanar da yan sanda yayinda suka zargi abinda yake yi.

Yace:

“Na yi karatu a Kwalejin kiwon lafiya da fasaha dake Kankia amma ban fara aiki ba. Yan bindigan na zuwa shagona don neman taimako kuma su biya ni.”

Yace yana sane da cewa yan bindiga ne saboda suna zuwa da bindigoginsu, amma babu yadda ya iya da su.

Ya bayyana cewa “yayi nadamar abinda yayi kuma ba zai sake ba.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here