Kwamitin Karba-Karba: Gwamnonin PDP za su yi Taro a Ranar Laraba, 29 ga Watanan

 

Gwamnonin PDP sun sanar da cewa kwamitin raba kujerar takara da Gwamna Ifeanyi Ugwanyi ke jagoranta ta shirya wata ganawa gabanin babban taronsu na kasa.

Rahotanni sun bayyana cewa, tuni aka aika da takardar sanarwar ganawar ga gwamnonin kafin babban taronsu.

Rahoton ya ci gaba da nuna cewa membobin jam’iyyar sun rarrabu kan batun raba mukamin shugabancin jam’iyyar na kasa, yana mai cewa ana ci gaba da tattaunawa.

FCT, Abuja- Gwamnonin Jam’iyyar PDP za su yi taro a ranar Laraba, 29 ga Satumba, a Abuja, don bayar da gudunmawa a shawarwarin da kwamitin karba-karba na Gwamna Ifeanyi Ugwanyi ya gabatar gabanin babban taron kasa na ranar 30 zuwa 31 ga Oktoba.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa a ranar Litinin, 27 ga watan Satumba, an aika da sanarwar ganawar ga dukkan gwamnonin da ake sa ran za su kasance a Abuja don muhimmin taron.

Jaridar a baya ta ruwaito cewa wata takarda da aka fallasa ta nuna cewa kwamitin karba-karban ya raba ofishin Shugaban jam’iyyar na kasa zuwa Kudu sannan ya mika ofishin sakataren jam’iyyar na kasa zuwa Arewa.

Wannan ya haifar da zanga–zanga daga membobin jam’iyyar na Kudu maso Gabas wadanda suka yi tsammanin za a karkatar da kujerar shugabancin jam’iyyar zuwa Arewa don ba Kudu damar samar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Wani mamba a kwamitin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce:

“Har yanzu ana ci gaba da tattaunawa.

“Duk abin da muka amince da shi a karshe bayan tattaunawa da gwamnoninmu a ranar Laraba, za a gabatar da shi ga Kwamitin Aiki na Ƙasa wanda shi kuma zai kai shi ga Kwamitin Zartarwa don tabbatarwa.”

Hakanan, ana sa ran taron na gwamnonin PDP karkashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jahar Sokoto zai tattauna batun kwamitin sulhu da Sanata David Mark ke jagoranta kan wasu batutuwan da suka shafi kalubalen shugabanci a jam’iyyar, Daily Trust ta rawaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here