Sojoji Sun Zane Mata ‘Yan Shi’a a Hanyar Abuja Zuwa Kaduna

 

Sojoji sun tare wasu motocci sun kama ‘yan Shi’a a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Wasu da abin ya faru a idonsu sun magantu kan yadda sojojin ke binciken motocci.

Rahotanni sun ce sojojin sun yi wa wasu mata ‘yan Shi’a bulala sannan suka tafi da su.

Abuja – Sojoji sun yi wa wasu mata ‘yan kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) da aka fi sani da shi’a duka a hanyar Abuja zuwa Kaduna a safiyar ranar Talata, Daily Trust ta rawaito.

Sojojin da suka kafa shinge a wani wuri a babban titin sun tare wani mota da ke dauke da matan.

Nan take bayan fitowarsu daga motar, sojojin suka yi wa matan bulala tare da haurin su.

Daga bisani aka tafi da su cikin wani mota da aka yi parkin din ta a gefe.

Wakilin Daily Trust, wanda ke wurin da abin ya faru ya ce ya gano jami’an tsaro suna razana wasu fasinjojin da mutane da ke wucewa.

Sojojin suna bincika motocin da nufin neman mambobin kungiyar ta IMN.

“Ku fito yanzu! Kai ma daya daga cikinsu ne!” wani kakarfar soja mai girman jiki ya tsawatawa wani mutum da ke cikin motar bas.

Shaidan gani da ido ta tabbatar da afkuwar lamarin

Wata mata da ta nemi a sakayya sunanta, ta ce tana tare da wasu ‘yan uwanta biyu a hanyarsu na zuwa tashar mota na Jabi a lokacin da aka tilastawa wasu fasinjoji da ke cikin motarsu fitowa.

Ta ce:

“Kafin mahaifiyata ta hau motar, an tilastawa direban da ya yi gaba. Ba mu samu damar taimaka mata ba sai dai kuka domin ba mu san halin da za ta shiga ba.”

Daily Trust ba za ta iya tabbatar da adadin mutanen da aka kama ba a yanzu da ake hada rahoton.

Duk da haramta taro da tattaki da gwamnati ta yi wa ‘yan Shi’a a Abuja, mambobin kungiyar suna cigaba da tattaki a titunan babban birnin kasar lokaci zuwa lokaci.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here