Rundunar ‘Yan Sandan Jahar Kano ta Kama Mai Garkuwa da Mutane Tare da Bindigu 2 ƙirar AK-47
Rundunar yan sandan jahar Kano ta bayyana cewa ta kama wani mutumi da ake zarginsa da aikata laifin garkuwa da mutane.
Yan sandan sun sami bindigu har guda biyu AK-47 a wurin wanda suka kama ɗin, amma ya ce ba nashi bane a hannun wasu yan Zamfara ya same su.
Mai magana da yawun hukumar yan sanda ta jahar Kano ya tabbatar da kama wanda ake zargin amma ya ce zasu gurfanar dashi a kotu zarar sun gama bincike Hukumar yan sanda a jihar Kano ta kama wani da ake zargin ɗan garkuwa da mutane ne, Abubakar Burumburum ɗan kimanin shekara 27.
Jami’an yan sanda na ‘Operation Puff Adder’ sun kama mutumin da bindigu guda biyu ƙirar AK-47, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Read Also:
Mai magana da yawun yan sandan jahar, DSP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da kama wanda ake zargin ga manema labarai ran Lahadi.
Haruna ya ce mutumin da aka kama, wanda aka fi sani da suna Likita a yankin Birnin Gwari, yana gudanar da aikinsa a jahohin Kano, Kaduna da sauran sassan arewa maso yamma.
A lokacin da yake amsa tambayoyi, Burumburum, wanda uba ne mai ‘ya’ya shida a karamar hukumar Tudun Wada, jahar Kano, ya amsa laifinshi da cewa yana satar shanu amma ya taɓa yin garkuwa da mutane sau biyu kacal.
Burumburum ya ce, bindigun da aka samu a hannunshi guda biyu kirar AK-47 ya same su ne a wajen ‘ya’yan wani mutumi da ya rasu, Muhammadu Bakanoma, a jahar Zamfara.
Sai dai mai magana da yawun yan sanda ya ce bada jimawa ba zasu gurfanar da Burumburum a gaban ƙuliya da zarar sun gama gudanar da bincike.