‘Yan Sandan Jahar Ogun Sun Kama Masu Garkuwa da Mutane 2

 

Rundunar ‘yan sandan jahar Ogun ta kama masu garkuwa da mutane 2 yayin amsar kudin fansa.

Dama mahaifin yaron da su ka sata mai shekaru 7 ya kai mu su korafi tun bayan sace shi da su ka yi da tsakar dare.

Jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin.

Ogun – Rundunar ‘yan sandan jahar Ogun ta samu nasarar damkar masu garkuwa da mutane 2 su na tsaka da amsar kudin fansar yaro dan shekara 7, kamar yadda The Punch ta rawaito,

Jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Litinin inda ya ce sun kama wani Muhammed Abubakar mai shekaru 42 da Clinton Niche mai shekaru 18.

Hakan ya biyo bayan korafin da aka kai ofishin ‘yan sandan na Agbara

Oyeyemi ya ce mahaifin yaron, Stephen Ajibili, ya kai korafin satar dan sa, Daniel, da aka yi inda ya ce mahaifiyar sa tana tsaka da aiki da misalin karfe 11:20am aka sace shi.

Ya kara da bayyana cewa mahaifin yaron ya bayyana mu su yadda masu garkuwa da mutanen su ka kira kuma su ka bukaci kudin fansa N1m.

Kamar yadda The Punch ta rawaito, ya ce:

“Bayan an kai rahoton, kwamandan ‘yan sandan yankin Agbara, CSP Kayode Shedrack, ya yi gaggawar tattara rundunar ‘yan sanda don su yi gaggawar bincike da daukar mataki akan lamarin.

“Kokarin ‘yan sandan ya haifar da da mai ido don masu garkuwa da mutanen sun bukaci iyayen yaron su kai kudin fansa daga nan aka dana musu tarko.

“Daga nan ne ‘yan sanda su ka tasa keyar su har sai da su ka nuna musu inda su ka daure yaron a cikin daji.

“Yayin tambayar wadanda ake zargin, sun sanar da ‘yan sanda cewa su 3 ne, dayan ya na kula da inda aka daure yaron ne yayin da su kuma su ka je amsar kudin fansa.

“Bayan fahimtar an kama mutane 2 daga cikin su, daya ya ba hammatar sa iska take yanke.”

Jami’in hulda da jama’an ya ce mukaddashin kwamishinan ‘yan sandan jahar, DCP Abiodun Alamatu, ya bayar da umarnin yin gaggawar mayar da wadanda ake zargin zuwa yankin yaki da garkuwa da mutane na bangaren binciken sirri na laifuka manyan laifukar rundunar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here