Rundunar ‘Yan Sandan Jahar Kano ta Kama Mutane 3 da Laifin Kwace Waya da Kashe Mutum
Rundunar ‘yan sandan jahar Kano ta kama wasu mutane 3 bisa zargin su da halaka wani Mohammed Sulaiman sannan suka tsere da wayar sa.
Bayan sun ji lugude ne su ka bayyana cewa tabbas sun kara kai wa wani Kingsley Sunday farmaki sannan suka yi awon gaba da wayar sa.
A ranar 20 ga watan Satumba kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana yadda lamarin ya faru a wata takarda.
Jahar Kano – Rundunar ‘yan sanda ta jahar Kano ta kama wasu mutane 3 da ake zargin sun sharba wa wani Mohammed Sulaiman wuka inda hakan ya kai ga ajalin sa sannan suka gudu da wayar sa.
Kamar yadda LIB ta rawaito, sun kara da bayyana cewa sun kai wa wani Kingsley farmaki a ranar Lahadi inda suka kwace wayar sa kuma suka tsere.
Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa a wata takarda ta ranar Litinin, 20 ga watan Satumba ya ce sun kama wadanda ake zargin bisa laifin fashi da makami.
Kamar yadda LIB ta ruwaito Kiyawa ya bayyana cewa:
“A ranar 19 ga watan Satumban 2021 da misalin karfe 11 na dare muka samu rahoton wasu batagari sun kai wa wani Mohammed Sulaiman mazaunin Sharada Quarters a Kano a daidai titin Yahaya Gusau dake Sharada inda suka datse shi da wuka kuma suka tsere da wayar sa.”
Read Also:
“Take a wurin aka wuce da shi asibitin kwararru na Murtala Mohammed inda aka tabbatar da rasuwar sa. Har ila yau, a ranar aka samu rahoton yadda da misalin karfe 11:20 na dare bata gari suka kara kai wa wani Kingsley Sunday mazaunin Panshekara Quarters dake Kano farmaki inda suka datse shi a kafadar sa suka tsere da wayar sa. An nufi asibitin Murtala da shi inda aka duba lafiyar sa kuma aka sallame shi.”
Kwamishinan bai bata lokaci ba ya tura rundunar ‘yan sanda su kama su
Bayan samun rahoton ne kwamishinan rundunar ‘yan sandar jahar, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ya tayar da wata runduna wacce SP Sulaiman Ibrahim ya jagoranta suka kama wadanda ake zargin.
“Cikin dabara rundunar ta kama Hussaini Malami mai shekaru 17, Harisu Manniru mai shekaru 20 da kuma Hussaini Abubakar mai shekaru 19 duk mazauna Zawaciki Quarters dake karkashin karamar hukumar Kumbotso a jahar Kano. An ga wuka mai alamar jini da kuma wayoyin wadanda su ka kai wa farmakin a wurin su.
“Bayan bincike mai yawan gaske wadanda ake zargin sun bayyana cewa sun kai wa Kingsley farmaki kuma sun datse shi a kafada da goshin sa kuma suka yi awon gaba da wayar sa. Sun kuma bayar da bayanai masu amfani.”
Kwamishinan ya ce za a dauki mataki a kan su
Kwamishinan rundunar ya ce za a mayar da lamarin zuwa bangaren binciken manyan laifuka don cigaba da bincike akan su sannan kotu ta yanke mu su hukunci.