Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta Kama Mutane 198 da Ake Zargin ‘Yan Ta’adda ne

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana kame wasu mutum 198 da ake zargin ‘yan ta’adda ne.

An gurfanar da wasu daga cikin ‘yan ta’addan da aka kama a ayyukan sintiri daban-daban na jami’an tsaro.

Yankin Arewa maso Yammacin Najeriya na daga cikin yankunan da ke fama da matsanancin rashin tsaro a Najeriya.

Jihar Kano – Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane 198 da ake zargi da aikata laifuka a jihar a tsakanin 27 ga watan Yuni zuwa 20 ga watan Yuli, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Samaila Dikko ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai kan nasarorin da rundunar ta samu a ranar Alhamis a Kano.

Ya ce 42 daga cikin wadanda ake zargin an kama su ne da laifin fashi da makami, tara kuma da laifin garkuwa da mutane, 16 da laifin damfara da kuma 27 masu satar motoci da masu satar babura uku.

Sauran wadanda ake zargin sun hada da 12 da ke safarar miyagun kwayoyi, da kuma tsageru 92 da aka fi sani da “Yan daba”.

Yadda aka kama su

Kwamishinan ya bayyana cewa, an kama wadanda ake zargin ne daga sassa daban-daban na jihar a ayyukan hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro, ‘yan sa kai da kai samame a maboyar ‘yan ta’addan.

Mista Dikko ya kara da cewa an gurfanar da wasu daga cikin wadanda ake zargin a kotu.

A cewarsa, ‘yan sanda sun kubutar da mutane biyar da aka yi garkuwa da su a lokacin da ake gudanar da aikin binciken.

Ya ce kayayyakin da aka samu daga hannun wadanda ake zargin sun hada da bindigu 25 da suka hada da AK-47 uku, motoci 12, keke napep guda bakwai, babura uku da kuma wukake 122.

Sauran kayayyakin sun hada da busassun ganye guda 269 da ake zargin tabar wiwi ne, wayoyin hannu 134, kwamfutar tafi-da-gidanka guda hudu, talabijin Plasma 16 da kayayakin bugarwa da dai sauransu.

Kwamishinan ya yabawa sauran hukumomin tsaro da kafafen yada labarai da kungiyoyin farar hula da masu ruwa da tsaki da ke taimakawa ayyukan ‘yan sanda a jihar.

Jaridar Tribune ta ba da lambobin wayan hukumar ‘yan sanda da za akira idan aka samu wasu bayanan tsaro; 08032419754, 08123821575, 08076091271 ko a sauke mahnyar “NPF Rescue Me” a sahar Play Store.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here