Zaɓen Edo: ‘Yansanda sun Kama Mutane Biyu Bisa Zargin Tayar da Tarzoma

 

‘da ke gudanar a yau Asabar.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan ƙasar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ranar Asabar, ya ce ‘yansandan sun kama mutanen biyu masu shekara 43 da 41 ranar Juma’a da maraice bayan da suka samu bayanan sirri cewa mutanen na shirin tayar da tarzoma a zaɓen na yau.

ACP Adejobi ya ce an kama su ne a mazaɓar Oredo, inda kuma bayan fara bincikarsu aka gano ƙananan bindigogin pistol ƙirar gida guda uku da wata babba guda ita ma ƙirar gida.

Ya ƙara da cewa ‘yansanda na ci gaba da riƙe mutanen biyu domin faɗaɗa bincike, inda ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

A yau ne dai al’ummar jihar Edo ke gudanar da zaɓen gwaman jihar.

Tuni dai dama rundunar ‘yansandan ƙasar ta ce ta girke jamai’ai kusan 35,000 domin tabbatar da zaman lafiya a lokaci da bayan gudanar da zaɓen.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here