‘Yan Sanda Sun Kama Wasu Samari da Ake Zargin Matsafa ne

An kama wasu samari 2 da ake zargin ‘yan damfara ne da akwatin gawa cike da ‘yan kamfan mata da rigunan nono a jihar Delta.

‘Yan sa kai ne suka fara kama samarin tukunna aka sanar da hukumar ‘yan sanda, wadanda suka yi gaggawar zuwa.

In ban da hukuma ta iso da wuri, da tuni mutane sun kashe samarin wadanda ake zargin matsafa ne.

Wasu ‘yan sanda da ‘yan sa kai da ke Ogwashi-Uku, karamar hukumar Aniocha ta kudu da ke jihar Delta, sun kama wasu samari 2 da akwatin gawa, cike da ‘yan kamfan mata da rigunan nono.

An kama wadanda ake zargin a wuraren Agidiehe quarters da misalin karfe 9:30 na daren Laraba, kamar yadda labarai suka bayyana.

Sai da ‘yan sa kai suka kama su tukunna aka sanar da ‘yan sanda. Kamar yadda wata majiya ta sanar, hankulan mata da samarin yankin sun yi matukar tashi sakamakon aika-aikan ‘yan damfarar yanar gizon.

Kamar yadda majiyar ta sanar, da tuni an kashe samarin in ban da ‘yan sanda sun bayyana da wuri. Ya kamata ace an tuhumesu akan yadda su kayi, su ka samo ‘yan kamfan mata da rigunan nonon da suka saka a akwatin gawar. Ya kamata hukuma ta hukunta su.

Jami’in hulda da jama’ar jihar, DSO Onome Onowakpoyeya, ta tabbatar da kamun samarin. A cewarta, ga dukkan alamu tsafi samarin za su yi da kayan, Vanguard ta ruwaito.

Onowakpoyeya ta ce sai da aka takura musu sannan suka bude akwatin gawar, inda suka ga ‘yan kamfai da rigunan nonon. Ta ce har yanzu ana cigaba da bincike a kan lamarin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here