‘Yan Sanda Sun Kashe ‘Dan Ta’adda a Sumamen da Suka Kai Sansanin ‘Yan Bindiga

 

Dakarun yan sanda sun kai samame sansanin yan bindiga a kauyen Anguwan Mai Zuma, ƙaramar hukumar Ɗanja a Katsina.

Rundunar yan sanda ta ce yayin samamen, Jami’ai sun sheke ɗan ta’adda ɗaya, sun kwato kayan aikin su da yawa.

Shugaban taawagar yan ta’addan, Sule Dawa, ya gudu da raunukan harsashi kuma yan sanda na bin diddiginsa.

Katsina – Rundunar ƴan sanda reshen jihar Katsina ta ce dakarunta sun hallaka ɗan ta’adda a ƙauyen Anguwan Mai-Zuma, a yankin ƙaramar hukumar Ɗanja.

Jaridar The Cable ta ce an kama Infoma da ke yi wa yan ta’addan aiki lokacin da gwarazan yan sanda suka kai samame yankin.

Mai magana da yaawun rundunar yan sandan, SP Gambo Isah, ya ce an yi kazamin artabu ranar 20 ga watan Agusta, 2022 tsakanin dakarun yan sanda da yan ta’addan a wani wuri da ake kira baƙin sansani a ƙauyen.

A cewarsa, gwarzan yan sandan sun kai samamen ne bayan samun wasu sahihan bayanan sirri kuma suka yi nasarar kakkaɓe yan ta’addan daga yankin.

Kakakin yan sandan ya ce bayanan da suka samu sun nuna cewa shugaban tawagar yan bindigan, Sule Dawa, ya tsere da harsasai a jikinsa. Gambo Isa ya ce:

“Jami’ai sun kwato abubuwa kamar bingidar gargajiya, kakin sojoji, Adda, Wuka, Kwalabe, Galan din wani abu da ake zargin kayan shaye-shaye ne, Baburan Boxer biyu, Keken ɗinki, Batiran Mota da sauran su a mafakar yan ta’addan.”

Rundunar yan sandan ta ƙara da cewa dakarun sun ƙara matsa kaimi da nufin cafke shugaban tawagar da sauran mayaƙansa.

Kwamishina ya yaba wa yan sanda

SP Isa ya ce kwamishinan yan sandan Katsina, Idrisu Dabban-Dauda, ya yaba da namijin kokarin jami’ai wajen ganin sun kawar da yan tada ƙayar bayan.

Kwamishinan ya bukaci dakarun yan sandan ka da su yi ƙasa a guiwa har sai sun tabbatar sun magance duk wani kalan aikata manyan laifuka.

Ya kuma roki al’umama da su cigaba da baiwa hukumomin tsaro haɗin kai a yaƙi da ta’addanci da ya addabi jihar Katsina, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here