‘Yan Sanda Sun Kashe Kasurgumin Ɗan Ta’adda, Dan Kundu

 

Jihar Katsina – Rundunar yan sanda ta sake hallaka wani rikakken dan ta’adda a jihar Katsina, Dan Kundu.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Dan Kundu kani ne ga kasurgumin dan bindiga, Usman Modi Modi.

Katsina: Yan sanda sun hallaka dan bindiga

Zagazola Makama ya tabbatar da haka a shafinsa na X a yau Asabar 21 ga watan Satumbar 2024.

An tabbatar da cewa Dan Kundu ya yi suna wurin addabar yankin karamar hukumar Safana a dajin Tsatskiya.

An yi nasarar hallaka Dan Kundu ne yayin arangama da jami’an yan sanda da kuma taimakon yan banga.

Kisan Dan Kundu ya faru ne a daren ranar Alhamis 19 ga watan Satumbar 2024 a kokarin kai hari a yankin Kurfi.

Jami’an tsaron sun yi nasarar dakile harin da suka yi niyyar kawowa da yaransa inda aka hallaka da dama.

Yadda aka hallaka Halilu Sabubu a Zamfara

Wannan na zuwa ne bayan kisan rikakken dan ta’adda, Haliliu Sabubu a ranar Juma’a 13 ga watan Satumbar 2024.

Kisan Sabubu ya yi wa yan Najeriya da dama dadi duba da yadda dan ta’addan ya addabi al’umma musamman a yankin Arewa maso Yamma.

“Bello Turji ya tsorata” – Sheikh Asada

Kun ji cewa Sheikh Murtala Bello Asada ya sake kalubalantar Bello Turji a wani bidiyo inda ya tabbatar da zargin ana daukar nauyin ta’addanci.

Malamin ya ce Turji a faifan bidiyo, ya tabbatar da hannun karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle wajen harkar ta’addanci.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan kisan rikakken dan ta’adda, Halilu Sabubu a Zamfara a ranar Juma’a 13 ga watan Satumbar 2024.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here