‘Yan Sandan Najeriya Sun Kashe Hatsabibin ‘Dan Fashin Daji a Neja
Rahotanni sun ce ‘ƴan sandan Najeriya sun Kashe wani jagoran ƴan fashin daji da ake kira Jauro Daji da kuma wasu mabiyansa ɓarayi a jahar Neja.
Jaridar PRNigeria da ke da kusanci da jami’an tsaron Najeriya ta ce majiyoyi daga rundunar ƴan sanda da suka tabbatar da lamarin sun ce an yi wa ƴan fashin ne kwantan ɓauna a daji kuma suka yi nasarar kashe kasurgumin ɗan fashin da mabiyansa.
An kuma kwato babura goma daga hannun ƴan fashin.
Read Also:
A cewar majiyar, ‘yan sandan sun yi amfani da sahihan bayanan sirri sannan suka yi wa ƴan fashin kwanton bauna a lokacin da suke ƙoƙarin tsallaka rafi a cikin daji.
Wani jami’in leken asiri da aka ambato ya ce: “Hadin gwiwar yan sanda da ƴan banga na yankin ne suka kashe Jauro Daji da kuma gungun ƴan fashinsa wadanda ke shirin yin garkuwa da mutane a wani ƙauye.
Majiyar ta ce Jauro Daji wanda ya sha jagorantar hare-hare a ƙauyuka da makarantu shi ke jagoranctar tawagar ƴan fashin masu yawa da ke kan babura.
Sannan an kai wa ƴan fashin harin ne a ranar Litinin tsakanin Gulbin Boko zuwa Dogon Fadama da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Kontagora a jahar Neja.