‘Yan Sanda Sun Kashe Mai Sana’ar Walda da Sunan ‘Dan IPOB ne a Jahar Imo
Wani wanda ya shaida faruwar wani lamari a jahar Imo ya bayyana yadda ‘yan sanda suka hallaka wani da sunan shi dan IPOB ne.
 Ya bayyana cewa, mutumin ya kasance mai sana’ar walda, kuma bai da alaka ta kusa ko ne sa da kungiyar IPOB.
 Rundunar ‘yan sanda ta fitar da sanarwar cewa, mutumin da jami’an ta suka kashe dan IPOB ne.
Daily Trust ta rawaito cewa, wani mazaunin jahar Imo, wanda ya shaida mutuwar Chigozie Nwaiwu, dan shekara 23 mai sana’ar walda, ya yi zargin cewa ‘yan sanda sun kashe shi tare da yi masa lakabi da jagoran IPOB.
 A cikin wata sanarwa da ta fitar a makon da ya gabata, rundunar ‘yan sandan ta ce Uchenna Chukwu na Umunakanu a karamar hukumar Ehime Mbano ta jahar Imo da wani abokinsa sun yi artabu da su.
A cewar jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan, CSP Mike Abattam, wanda ya fitar da sanarwar, mutanen biyu sun shiga hannun jami’an da suka kai hari a maboyarsu, a cikin artabun bindiga.
Amma da yake magana a wani sanannen shirin rediyo a garin Owerri, babban birnin jahar, wani shaida ya ce an kashe Chukwu haka siddan.
Shaidan ya ce:
 “Yaran biyu, Chigozie da Uchenna sun kasance abokai tun suna yara. Chigozie ya ziyarci Uchenna Chukwuanyanwu a shagonsa na walda.
 “Kwatsam, mota kirar Venza ta iso kuma mutanen da ke cikin motar suka game mai walda suka jefa shi cikin motarsu. Suna shirin tafiya sai Chigozie ya tambaye su dalilin da ya sa za su tafi da Uchenna.
 “Mutanen cikin motar da ke sanye da kayan gama gari sai suka harbi Chigozie a goshi. Motar ta yi tafiyarta, mutane sukataru don ganin abin da ya faru.
A cewarsa, daga baya motar ta sake dawowa, inda mutanen suka dauki gawar suka tafi da ita.
Ya kara da cewa, iyalan Chigozie da Uchenna sun shiga mamakin abin da ya faru.
Shaidan ya ce mutumin da ‘yan sandan suka zo kamawa Chidera ne, wani ma’aikacin aluminium, wanda ke da shago kusa da na Uchenna.
 SaharaRepoters ta rawaito shi inda ya kara da cewa:
 “An harbe Chigozie ne kawai saboda ya dage kan sanin dalilin tafiya da Uchenna. Babban abin haushin shine sanarwar da ‘yan sanda suka fitar.”
 “Sun sanya Uchenna a matsayin jagoran IPOB a Ehime Mbano, wannan karya ce tsagoranta don boye ayyukan su. Har yanzu zuciyata tana kuna, ban taba ganin irin wannan mugunta ba tun da aka haife ni.”
 Sai dai rundunar ‘yan sandan ta ce suna nan kan bakan su na cewa yaran sun kasance ‘yan kungiyar IPOB.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here