Ma’aikatan Hukumar ‘Yan Sanda Sun Tafi Yajin Aiki

 

Ma’aikatan Hukumar Jin Dadin Yan Sanda Watau Police Service Commission Sun Tafi Yajin Aiki.

Suna zargin Sifeton yan sanda IGP da yiwa dokokin hukumar katsalandan tare da watsi da hukuncin kotun daukaka kara.

Hukumar PSC ta kwan biyu tana sa’insa da Hukumar Yan sanda tun lokacin tsohon IGP Mohammed Adamu.

Abuja- Gamayyar ma’aikatan hukumar kula da yan sanda PSC ta sanar da tafiya yajin aiki ga shugabanta bisa saba alkawuran da akayiwa ma’aikatan.

Gamayyar ta bayyana cewa zasu fara yajin aikin ne ranar Litinin, 29 ga watan Agusta, 2022.

Shugaban gammayar, Mr Adoyi Adoyi, ya bayyana haka a hira da manema labarai ranar Alhamis a Abuja, rahoton Punch.

Ya ce sun yanke shawarar tafiya yajin ne sakamakon rashin jituwa dake gudana tsakanin shugaba hukumar, Musuliu Smith da Sifeto Janar na yan sanda, Usman Baba, lamarin daukan sabbin yan sanda, karin girma, dss.

Yace kara da cewa Sifeton yan sanda IGP gaba daya yana yiwa dokokin hukumar katsalandan tare da watsi da hukuncin kotun daukaka kara.

A cewarsa:

“Zamu tafi yajin aiki ne daga ranar Litnin, 29 ga Agusta, don nuna rashin amincewarmu da yadda Shugaban hukumarmu ke jagoranci da kuma sabawa umurnin kotu da Sifeto Janar IGP Usman Baba, ke yi.”

“Aikin hukumar PSC a bayyane yake amma a kundin tsarin mulki amma IGP duk ya yi watsi da su, ya kwace ayyukan hukumar. Shi ke nadin mutane kuma yake garin girma sabanin abinda doka ta tanada.”

“A bisa kundin tsarin mulki, nadin mukamai, karin girma, da daukan sabbin yan sanda duk aikin PSC ne ba IGP ba.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here