Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta Gudanar da Faretin Bankwana ga AIG Bishi

Babban jami’in dan sanda, Omololu Bishi, mai mukamin AIG ya yi mutuwar bazata bayan kara masa girma.

A ranar 18 ga watan Disamba, 2020, IGP Mohammed Adamu ya karawa marigayi AIG Bishi mukami zuwa AIG mai kula da makaman rundunar ‘yan sanda.

Rundunar ‘yan sanda a karkashin jagorancin AIG Ahmed lliyasu ta gudanar da faretin ban kwana da AIG Bishi.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gudanar da fareti mai kayatarwa domin bankwana da marigayi AIG Omololu Bishi, wanda aka binne gawarsa a Legas.

Marigayi Bishi, mai mukamin mataimakin Sufetan Ƴansandan Najeriya mai kula da makaman rundunar ƴan sanda a hedikwatar ta da ke Abuja, an binne shi a maƙabartar Ebony Vaults da ke Ikoyi.

AIG Bishi ya rasu ne ranar Litinin a wani asibiti da ke Ikeja, Legas, inda aka kwantar da shi bayan ya kamu da rashin lafiyar da ba’a bayyana ba.

Biyo bayan rasuwarsa ne babban sifeton rundunr ‘yan sanda, IGP Mohammed Adamu, ya bayar da umarnin a yi masa jana’izar karramawa ta musamman, kamar yadda Premium Times ta rawaito.

AIG na Zone 2, AIG Ahmed Iliyasu, shine ya jagoranci jami’an ƴan sanda a Lagos don wakiltar Babban Sufetan ƴan sanda, IGP Abubakar Adamu, wajen ƙaddamar da fareti don karrama Marigayin, babban Jami’in Rundunar.

Marigayin wanda ya tashi a tsibirin Legas (Lagos Island) ya samu ƙarin matsayi zuwa muƙamin mataimakin babban sifeta (AIG) a ranar 18 ga watan Disamba, 2020.

An ɗauke shi aiki a rundunar ƴansanda sanda a shekarar 1988 a matsayin ƙaramin mataimakin Sufiritandan ƴansanda.

Ya rasu ya bar mata da ƴa’ƴa.

AIG Ahmed Iliyasu, wanda ya jagoranci farenti karrama gawar marigayin, ya samu rakiyar Kwamishinan ƴan sandan Jahar, CP Hakeem Odumosu, Kwamandojin yanki,Ƴansandan kwantar da tarzoma da sauran manyan jami’an ƴansanda.

Jana’izar tasa ta samu halartar iyalansa, wakilan Sarkin Legas (Oba of Lagos), abokan aikinsa, ƴan uwa da sauran abokan arziƙi.

AIG Ahmed Iliyasu ya nuna kaɗuwarsa da mutuwar bazatar AIG Omololu Bishi,wanda ba’a daɗe da ƙara masa matsayi zuwa muƙamin AIG ba.

Ya bayyana jami’in a matsayin jajurtacce, mai ƙwazo, da aiki tuƙuru.

Ya yi ta’aziyya da jaje ga iyalan mamacin, Sarkin Lagos da abokansa bisa rasuwar Marigayi Bishi.

Ya yi addu’ar Allah ya basu haƙurin juriyar wannan rashin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here