Hukumar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi Sababbin Sauye Sauye da canza Wuraren Aiki ga Jami’anta
Hukumar yan sandan Najeriya ta sanar da sabbin sauye sauye a tsakanin jami’anta.
Rundunar ta sauya wa wasu kwamishinonin yan sanda wuraren aiki.
Har ila yau hukumar ta nada wasu jami’ai a sabbin matsayi.
Hukumar yan sandan Najeriya a ranar Laraba, 13 ga watan Janairu, ta sanar da turawa tare da sauya wa wasu jam’ai wuraren aiki zuwa hukumomin rundunar tara a kokarin yin sauyi a kasar.
Mataimakin jami’in hulda da jama’a, Aremu Sikiru Adeniran ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, a shafin sadarwa na rundunar.
Aremu ya ce sauyin zai fara aiki a nan take, inda ya kara da cewa dole dukkan jami’an da aka yi wa sauyi su koma sabbin tashoshinsu.
Jerin sunaye da matsayinsu sun hada da:
1. Jahar Kebbi – CP Adeleke Adeyinka Bode, mni
2. SPU, FHQ, Abuja – CP Philip Maku
Read Also:
3. Jahar Sokoto – CP Ali Janga Aji
4. Armament, FHQ, Abuja – CP Ohikere S. Idris, fsi
5. CMDT Police College Ikeja -CP Daniel Sokari-Pedro, mni
6. Port Authority Police (PAP), Western, Lagos – CP John O. Amadi, mni
7. Jahar Oyo – CP Ngozi Onadeko, fdc
8. Jahar Enugu – Mohammed Ndatsu Aliyu
9. Border Patrol, FHQ, Abuja – CP Haladu Musa Rosamson, fdc
10. Jahar Cross River – CP Sikiru Akande
11. Jahar Ebonyi – CP Aliyu Garba
12. Hukumar filin jirgin sama – CP Abubakar Umar Bature
13. Sashin ayyuka, FHQ – CP Yusuf Ahmed
14. Jahar Adamawa – CP Aliyu Adamu Alhaji
15. Sashin horo – CP Babaita Ishola 16. Jihar Imo – CP Nasiru Mohammed
18. Jahar Delta -CP Ari Mohammed Ali
19. Sashin yaki da ta’addanci, FHQ, Abuja – CP Olofu Tony Adejoh
20. Peacekeeping, FHQ, Abuja – CP Sadiq Idris Abubakar
21. Jami’in hulda da jama’a na rundunar – CP Frank Mba.