Manyan ‘Yan Siyasa 10 Masu Tasiri a Zabukan 2023 a Fadin Najeriya

 

Kasa da watanni biyar da suka rage zaben 2023, miliyoyin ‘yan Najeriya zasu damka makomarsu a hannun ‘yan siyasa inda zasu yi zaben sabon shugaban kasa da zai karba ragamar kasar.

Zaben Fabrairun 2023 na iya zama abinda zai kawo sauyin cigaba a fannin tattalin arziki da siyasar Najeriya wanda ta dade tana nema, Vanguard ta rahoto.

Idan muka hango shekarar zabe, bari mu duba manyan masu tasiri ga ‘yan Najeriya a siyasar da kuma masu rawar takawa.

Ga 10 daga cikin manyan masu tasiri a zabuken 2023 a fadin Najeriya:

Shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari har yanzu yana daga cikin manyan masu ruwa da tsaki a Najeriya kuma babu shakka zai goyi bayan Tinubu idan aka fara kamfen.

Zai so jam’iyyar APC ta cigaba da mulkin kasar nan don haka zai bai wa ‘dan takarar duk goyon bayan da ya dace ya samu don cin nasara.

Bola Ahmed Tinubu

‘Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC a zaben 2023, Bola Tinubu yana alfahari da rawar da ya taka a siyasa tun daga 1999, a matakin jiha da na tarayya.

Yanzu da yake neman kujera mafi daraja a kasar nan, Tinubu mai shekaru 70 yana kokarin janyo hankalin ‘yan Najeriya wurin nuna musu zai sauya akalar kasar.

Atiku Abubakar

Kamar Buhari, Atiku ya ki hakura da burinsa na zama shugaban kasar Najeriya. ‘Dan asalin jihar Adamawan ya nemi kujerar shugabancin kasa sau biyar.

A yanzu shi ne ‘dan takarar shugabancin kasa na PDP, babbar jam’iyyar adawa ta kasar nan kuma yana fatan zama shugaban kasa a takararsa ta shida.

Sanata Abdullahi Adamu

Sanata Adamu yayi nasarar zama shugaban jam’iyyar APC. Ya matukar taimakawa wurin zaben fidda gwanin jam’iyyar APC.

Gogewarsa a fannin mulki ya taimaka wurin gyara jam’iyyar duk da rikicin da ya kunno kai a wannan lokacin. Lauyan, manomin kuma tsohon ‘dan siyasan yanzu ya mayar da hankali wurin ganin nasarar Bola Tinubu.

Dumebi Kachikwu

Mutane da yawa sun sha mamaki lokacin da Kachikwu ya lallasa Kingsley Mogahku, Chukwuka Monye da wasu ‘yan takata takwas a zaben fidda gwanin ‘dan takarar shugaban kasa na ADC.

Tun bayan nan, ‘yan Najeriya sun mayar da hankalinsu kan ‘dan kasuwar da ke kafa sunansa cikin sauki a wurin masu kada kuri’a.

Peter Obi

Bayan takarar mataimakin shugaban kasa da yayi tare da Atiku a zaben 2019 da kuma kin yadda ya sake bayyana mataimaki a PDP, Obi ya bar jam’iyyar inda ya koma LP.

Tsohon gwamnan Anambran yana shan yabo daga jama’a masoyansa inda ake tsammanin zai tada kura duk da ba dole bane yayi nasara a zaben 2023.

Rabiu Kwakwanso

‘Dan takarar shugabancin kasan a karkashin jam’iyyar NNPP, Kwankwaso ya tabbata mutum mai maida hankali da karfin neman abinda yasa gaba.

Tsohon gwamnan Kanon ya shiga tsakiyar manyan ‘yan takara shugabancin kasa a zaben Fabrairun 2023 kuma yana cigaba da bayyana karfin guiwar nasara.

Sanata Aishatu Ahmed Binani

Ita ce mace ta farko ‘yar takarar gwamna a jihar Adamawa inda mai shekaru 51 ta lallasa Nuhu Ribadu da tsohon gwamna Bindow kuma tayi wuf da tikitin jam’iyyar.

Wannan kadai zai bayyana irin karfin guiwar da take da shi da kuma farin jininta a wurin jama’ar Adamawa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here