Yadda ‘Yan Siyasar Kudu za su bi, su Karbi Shugabanci a Zaben 2023 – Shehu Sani

 

Shehu Sani yace tsari na karba-karba zai taimaka wajen kawo adalci a siyasa.

Amma Sanatan ya bayyana cewa ba dole ba ne mulki ya bar Arewa zuwa Kudu.

‘Dan siyasar yace idan aka ce da barazana za a ci zabe a 2023, ba za ayi nasara.

FCT, Abuja – A wata hira da Legit.ng Hausa, Sanata Shehu Sani, ya yi magana game da siyasar 2023, da yadda ‘yan siyasar kudu za su bi, su karbi shugabanci.

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya zanta da Legit Hausa, ya kuma bayyana cewa ba zai yiwu mulki ya bar Arewa da karfa-karfa da barazana ba.

Kwamred Shehu Sani yace kafin mulki ya zo Arewa, sai da ‘yan siyasar yankin suka samu ‘yan kudu, suka hada-kai, sannan suka nemi kuri’un talakawa a 2015.

“Adalci ne ya kasance mulki yana yin Kudu, ya na yin Arewa. Amma ba tilas ne a damukaradiyya ba.”

Abin da ya kamata ‘Yan kudu su yi

“Tun da ba doka ce ta damukaradiyya ba, ana iya cin ma burin ne ta hada-kai, da lalama da nuna ta haka ne za a samu zaman lafiya.”

“Idan gwamnonin Kudu suna son mulki daga Arewa, abin da za su yi; jawo ‘yanuwansu na Arewa, su zo Arewa, ayi tare, a hada-kai.”

Shehu Sani yake cewa dole ne ‘yan siyasan yankin Kudu suyi kokarin nuna wa mutanen Arewa fa’idar mulki ya koma hannunsu a babban zabe mai zuwa na 2023.

“Idan za ayi shi ne da barazana, to ba za a samu nasara ba.”An yi wata yarjejeniya a 2015?

Da aka tambayi Shehu Sani ko ya san wata yarjejeniya da aka yi tsakanin Muhammadu Buhari da ‘yan siyasar Kudu kafin APC ta hau mulki, sai yace bai da labari.

“To shi dai alkawari idan aka yi shi, ana bukatar abubuwa biyu; shaida na mutane, kuma da na rubutu.”

“Ni dai ban san maganar karba-karba da aka yi ba, saboda su kansu, ba su san cewa za a iya cin mulki a lokacin ba.

Sani yace abin da ya sani shi ne, ba don bangaren Yarbawa ba, da Buhari bai zama shugaban kasa ba, idan za ayi adalci shi ne suma su karrama abin da aka yi masu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here