‘Yan Ta’adda, ‘Yan Fashin Daji da ‘Yan Tada Kayar Baya Basu da Mafaka a Faɗin ƙasar Nan – Gwamnatin Buhari
Abuja – Gwamnatin tarayyan Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, tace taɓarɓarewar matsalar tsaro ta kare. Ta ce yan ta’adda na kokarin guduwa amma ba zasu tsira ba.
Read Also:
The Nation ta ruwaito gwamnatin tarayya na cewa ‘yan ta’adda, yan fashin daji da duk wasu gungun yan tada kayar baya basu da mafaka a faɗin ƙasar nan.
Ta ƙara da cewa ‘yan Najeriya ka iya ganin ‘yan tsirarun Kes ɗin matsalar tsaro nan da can amma ba zai yi muni kamar yadda ta faru a baya ba.
An bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai na Ministoci huɗu tareda babban Hafsan tsaro na ƙasa, Janar Lucky Irabor.
Ministocin sun haɗa da Alhaji Lai Muhammed (Yaɗa labarai), Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya (Tsaro), Rauf Aregbesola (Cikin gida) da Mohammed Maigari Dingyadi (Harkokin yan sanda).
Ku dakaci ƙarin bayani…