Meyasa Zan Saci Kudin Jama’a Alhali na fi Shugaban Amurka Arziki – Peter Obi

 

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour ya yi wasu lafuzza dangane da kudaden jihar Anambra a lokacin da yake gwamnan jihar.

A baya dai Peter Obi ya ce, idan kudaden da ya mallaka na al’umma ne ya sata to kada Allah ya barshi, ya hukunta shi tun a duniya.

A wannan karon, ya ce shi fa ba talaka bane, domin kuwa yana da kudaden da suka haura na shugaban kasar Amurka Joe Biden.

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya bayyana asalin dalilin da ya sa ba zai taba iya sace kudin gwamnati ba.

A cewar tsohon gwamnan na jihar Anambra, Allah ya albarkace shi; don haka ba shi da bukatar satar ‘kudin jama’a’.

A faifan bidiyon dake yawo a shafin Twitter, Obi ya ce idan ya taba cin kudin al’umma to kada Allah ya bashi natsuwa.

Na fi Joe Biden kudi, inji Obi

Obi ya yi alfahari da cewa ba zai taba kudin al’umma ba, domin Allah ya bashi arziki iya yadda yake bukata.

Don haka, Obi ya ce yana wajen lokacin da shugaban kasar Amurka Joe Biden yace yana da kudin da basu wuce $8.9m.

Ya ce shi, a matsayinsa na dan Najeriya kuma kasar da ake ganin mai fama da fatara to ya mallaki abin da shugaban na Amurka bai mallaka ba, don haka ba shi ba sata.

A kalamansa:

“Shugaba Biden ya mallaki dalar Amurka miliyan 8.9, meye yasa wani kamar ni daga wata kasa a duniya ta 3 zai saci kudin jama’a alhali na fi shugaban na Amurka arziki.”

Ya ce shi ba burinsa bane ya mallaki jirgi mai zaman kasan ko katafaren gida ba, burinsa kawo sauyi ne a Najeriya.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here