‘Yan Ta’adda Sun Kashe Shugaban Jam’iyyar APGA na Gunduma a Jihar Ebonyi

 

Kwana kaɗan kafin zabe, yan ta’adda sun kashe shugaban APGA na gunduma a jihar Ebonyi, kudu maso gabashin Najeriya.

Wani ɗan uwan mamacin ya ce lamarin da ɗaga hankali ganin yadda suka fito da shi yana cikin bacci jiya da daddare.

Wani masoyin jam’iyyar APGA ya ce marigayi Idoko mutun ne nai neman na kansa da kokarin taimaka wa al’umma.

Ebonyi – Wasu yan bindiga da ba’a sani ba sun halaka shugaban jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) na gudumar Ohofia Agba, Mista Monday Idoko, a karamar hukumar Ishielu, jihar Ebonyi.

Jaridar Vanguard ta ce maharan sun harbe shi a tsakiyar ka a mahaifarsa ƙauyen Onueke, yankin Ohofia-Agba da misalin karfe 11 na daren jiya Laraba.

Wani ɗan uwan Mamacin, wanda ya yi magana cikin hawayen bakin ciki kuma ya nemi a sakaya bayanansa, shi ne ya tabbatar da lamarin ga manema labarai ta wayar salula.

Ya ce makasan sun kutsa cikin kauyen kana suka zakulo shugaban jam’iyyar wanda ya riga ya fara bacci, suka harbe shi a kai, nan take rai ya yi halinsa.

Ya ce:

“Ɗan uwana, labarin akwai tashin hankali, wani ɗan gidanmu ya sanar da ni cewa wasu mutane ɗauke da bindigu suka kutsa gidan da suke kwance kafin dare ya raba.”

“Suka fito da ɗan uwana daga bisani suka bindige shi a kai, sun yi kokarin garzayawa da shi Asibiti amma rai ya yi halinsa tun a cikin kauyen. Muna cikin yanayin jimami tun jiya.”

Wani mamban APGA wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce marigayi Idoko ya maida hankali wajen shirye-shiryen zuwa ɗan takarar gwamnan APGA, Benard Odoh, kafin a kashe shi.

Ya ayyana marigayin da mutum mai dogaro da kai wanda ya sadaukar da komai nasa domin ci gaban jam’iyyar APGA da al’ummar yankinsa, kamar yadda Leadership ta rahoto.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here