‘Yan Ta’adda Sun Kai wa Jahar Borno Farmaki, Sun Saci Kayan Tallafi Tare da Kona Wasu

 

‘Yan ta’adda sun saci wasu kayan tallafi sannan suka bankawa wasu wuta a Damasak, jahar Borno.

Kamar yadda NWC ta tabbatar, wannan karo na biyu kenan cikin watanni biyu da irin wannan lamari ya faru.

Darektan NRC na Najeriya, Eric Batanon, ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce ma’aikata 5 sun tsere da kyar ‘Yan ta’adda sun kaiwa kayan tallafi a Damasak, jahar Borno farmaki kamar yadda NRC ta tabbatar.

Sai da suka saci na sata sannan suka bankawa sauran wuta a ma’ajiyarsu. Kamar yadda The Cable ta ruwaito, dama sun taba kai farmakin a karo na biyu kenan a arewa maso gabas, sannan karo na hudu kenan a Damasak da kewaye.

Darekatan NRC na Najeriya, Eric Batonon, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace ma’aikatan wurin guda 5 sun tsira.

‘Yan bindigan sun dade suna kaiwa ma’aikata da kayan tallafin hari tsawon shekaru wanda hakan abu ne mai muni ga harkar tallafin a arewa.

Batonon ya ce wadannan hare-haren suna janyo matsala ga harkar tallafi a Najeriya don haka yayi kira ga gwamnatin Najeriya da tayi iyakar kokarin bayar da tsaro da kulawa ga ma’aikatan yankin da kayan aikinsu.

“Mummunan harin da ya faru a jiya ya jika mana aiki kuma ya firgita rayukan ma’aikatanmu da dama. Mun godewa Ubangiji da har ma’aikatanmu 5 da suke zama a Damasak suka kubuta ba tare da wani abu ya samesu ba,” a cewarsa.

“Maharan sun yi nasarar bankawa ma’ajiyarmu wuta tare da lalata kayan tallafawa rayuwar jama’a har da ababen hawan direbobinmu.

“Mun yi Allah wadai da wannan aikin banzan. Daga zuwa taimako sai su dakatar damu daga cimma manufarmu.

“Hanyoyin taimakon al’umma suna ta ragewa a arewa maso gabas ta Najeriya, don haka muke rokon gwamnatin Najeriya da ta agaza mana da taimako.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here