‘Yan Ta’adda na Fito da Sabbin Dabarun Hare-Hare a Arewa Maso Yamma da Arewa ta Tsakiya

 

Rundunar sojojin Najeriya ta fitar da wata sanarwa inda take cewa wasu ‘yan ta’adda da ke kai hare-hare a shiyyar arewa maso yamma da arewa ta tsakiya na amfani da wasu hanyoyin yaudara da za su iya kai wa ga tayar da rikici a ƙasa.

Bayanin ya ƙara da cewa akwai hujjojin da ke nuna cewa ‘yan ta’addan na amfani da dabarun dasa nakiya da sauran abubuwa masu fashewa wajen kai hare-hare, abin da zai jefa tsoro cikin zukatan mutane.

Sai dai rundunar sojojin ta ce a shirye take domin bankaɗo duk wani makirci da ‘yan ta-da-ƙayar-bayan ke amfani da shi, duk girmansa.

Babban hafsan sojojin Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a a hedkwatar Sojoji da ke Abuja, lokacin da yake karɓar baƙuncin mai taimaka wa Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya a kan sha’anin yaƙi da ta’addanci, Vladimir Voronkov.

Babban hafsan sojojin ya kuma ce a shirye rudunar take don yin haɗin gwiwa da Majalisar Ɗunkin Duniyar wajen ganin an maido da zaman lafiya a yankunan ƙasar.

Ya ce za su yi amfani da kowanne mataki da ya dace domin tabbatar da nasarar hakan.

Ya kuma nemi tallafin Majalisar Ɗinkin Duniyar da sauran hukumomi domin ɗaukar matakin da ya fi dacewa ga tubabbun ‘yan ta-da-ƙayar-baya.

Mai taimakawa Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Vladimir Voronkov, ya sha alawashin cewa hukumarsa za ta tallafawa Najeriya wajen gano da kuma gurfanar da masu aikata muggan laifuka.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com