An Kashe ‘Dan Sanata Bala Na ALLAH, a Gidansa Dake Kaduna

 

An gano gawar babban dan Sanata Bala Na Allah, Kyaftin Abdulkarim Bala Na Allah, a dakin kwanansa da ke Malali a jahar Kaduna.

‘Yan ta’adda sun kashe dan sanatan jahar Kebbi a cikin gidansa Lahadi, Agusta 29, 2021 at 7:09 Yamma by Salisu Ibrahim An gano gawar babban dan Sanata Bala Na Allah, Kyaftin Abdulkarim Bala Na Allah, a dakin kwanansa da ke Malali a jahar Kaduna.

Daily Trust ta tattaro cewa matukin jirgin mai shekaru 36, wanda ya yi aure kwanan nan, an daure shi kuma kana aka shake shi har ya mutu yayin da maharan suka tsere da motarsa ​​da kayayyakinsa.

Mai ba da shawara na musamman ga Sanata Na Allah, Garba Mohammed, yayin tabbatar da mummunan abin da ya faru, ya ce maharan sun samu shiga gidan ne ta rufin bayan gidansa.

Ya ce wani mai gadin makwabcinsa ya lura da cewa an bude kofar gidan marigayin tare da yin alama wanda ya kai ga gano gawar matukin.

An rawaito cewa Sanata Na Allah, wanda a halin yanzu baya Najeriya, yana da ‘ya’ya uku wadanda dukkansu matukan jirgi ne.

Da yake magana da wakilin Daily Trust, Mohammed ya ce za a yi sallar jana’izar marigayin a Yahaya Road yayin da za a bunne shi a makabartar Unguwan Sarki.

Rundunar ‘yan sandan jahar Kaduna har yanzu ba ta mayar da martani kan kisan ba amma Mohammed ya shaida cewa an sanar da ‘yan sanda kuma a halin yanzu suna wurin da kisan ya faru.

Bala Na’Allah yana wakiltar Kebbi ta Kudu a majalisar dattawa.

Karin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here