Mutane 3 Sun Mutu a Harin da Sojojin Amurka Suka Kai Afghanistan

 

Amurka ta kai hari kan wani mutum da ta yi zargin dan kunar bakin wake ne a Afghanistan.

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki kadan da aka samu wata fashewa a filin jirgin Kabul.

Rahoto ya bayyana cewa, mutane uku sun mutu ciki har da mace da kuma yaro karami.

Afghanistan – Sojojin Amurka sun kai hari da jirgi mara matuki kan wani mutum da ta ce mai shirin kunar bakin wake ne na ISIS-K a lardin Nangarhar da ke gabashin Afghanistan, a yayin da ake gargadin yiwuwar kai sabbin hare-hare wajen kokarin kwashe Amurkawa daga Kabul.

Manufar yunkurin jigilar kwashe Amurkawa da ‘yan Afghanistan wadanda suka taimaka wa sojojin Amurka da jami’ai daga kasar zuwa karshen watan nan ya zo karshe.

A cewar mazauna yankin da aka kai harin a daren Juma’a, akalla mutane uku sun mutu – namiji, mace da yaro – kuma mutane da dama sun jikkata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here