PDP ce kadai za ta Iya Samar da Madaidaiciyar Mafita Kuma ta Kafa Ingantaccen Shugabanci a Najeriya – Shugaban Matasan Arewa

 

Kungiyar shugaban matasan Arewa sun bukaci Obasanjo ya nemo mafita ga ‘yan Najeriya.

Kungiyar ta bukaci shugaban da ya yi kira ga taron iyayen kasa domin samar da mafita ga kasar.

Sun kuma bukaci ya ayyana PDP a matsayin jam’iyyar da za ta iya kawo mafita ga ‘yan kasar.

Abeokuta, Ogun – Kungiyar Shugabannin Matasan Arewa (NYLF), wata kungiyar gamayyar kungiyoyin Arewa 42, ta yi kira ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da ya gaggauta kiran taron “Iyayen Najeriya” da nufin shiga tsakani a matsalolin kasar da kuma samar da mafita.

Kungiyar musamman ta yi kira ga Obasanjo da ya shiga tsakani a rikicin da ke kara ta’azzara a jam’iyyar PDP, tare da bayyana cewa jam’iyyar ita ce kadai fata ga ‘yan Najeriya, Sun News ta tattaro.

Ta kuma bayyana Obasanjo a matsayin “gogaggen dan kasa wanda ya yi imani da gamayyar Najeriya.” Shugaban NYLF na kasa, Elliot Afiyo, ya yi wannan kiran ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Abeokuta, jahar Ogun, jiya, jim kadan bayan ganawarsa da Obasanjo.

Afiyo, wanda ya ambaci wasu ‘Iyayen Najeriya’ da suka hada da tsohon Shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida (mai ritaya), Janar Theophilus Danjuma (mai ritaya) da Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya) da Ernest Shonekan.

Kungiyar ta lissafo matasalolin Najeriya da suka gada da ‘yan bindiga, yawan garkuwa da mutane, cin hanci da rashawa, barakar tattalin arziki, tashe-tashen hankula daga ‘yan aware da dai sauran matsalolin da sauka dabaibaye kasar.

Ya ce lokaci ya yi da wadannan “‘yan Najeriya masu kishin kasa” za su hadu su kuma samar da mafita ga kalubalen da ake fuskanta kafin su dulmuye kasar.

Shugaba Buhari ya kasa cika burin ‘yan Najeriya

Ya bayyana cewa NYLF tana cikin kungiyoyin da suka marawa shugaba Muhammadu Buhari baya a 2015, amma yayi nadamar cewa shugaban kasar ya kasa cika burin ‘yan Najeriya.

Ya zargi APC da rashin kwarewa a siyasa wajen magance dubban kalubalen da ke fuskantar kasar.

A cewarsa, PDP ce kadai za ta iya samar da wata madaidaiciyar mafita kuma ta kafa ingantaccen shugabanci da ‘yan Najeriya ke fata nan gaba.

Musabbabin rikicin da ya dabaibaye PDP

Ya ce rikicin da ya dabaibaye PDP ya samo asali ne sakamakon nuna ikon mulki tsakanin wasu gwamnoni saboda burinsu na shugabancin kasa a 2023.

Da yake magana kan barakar neman canjin mulki kafin shekarar 2023, Afiyo ya ce shugaban na gaba zai iya fitowa daga kowane bangare na kasar, muddin dan takarar yana da cancanta da karfin da zai magance matsalolin Najeriya.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here