‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 2 a Jahar Kaduna

A wani sabon harin ‘yan bindiga, an hallaka mutane biyu tare da jikkata wasu a Kaduna .

Sojoji sun kuma ceto wasu mutane uku matafiya a wata hanyar a Kaduna bayan an sace su.

Gwamna El-Rufai ya yi Allah wadai da harin, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan mamatan.

‘Yan bindiga sun hallaka mutane biyu a kauyen Makoro Iri dake karamar hukumar Kajuru ta jahar Kaduna.

A cewar wani rahoton tsaro, ‘yan bindigar sun mamaye kauyen inda suka harbe mutane biyu da aka bayyana sunayensu da Gideon Mumini da Barnabas Ezra, Daily Trust ta rawaito.

Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi 29 ga watan Agusta.

Sojoji sun ceto matafiyan da aka sace

A wani labarin kuma, rundunar Operation Safe Haven ta ceto matafiya uku daga hannun ‘yan bindiga a hanyar Gidan Waya zuwa Godogodo a karamar hukumar Jema’a.

‘Yan bindigan da suka tare hanya sun sace matafiya.

Sojoji sun amsa kiran gaggawa sannan sun bi ‘yan bindigan, inda suka kubutar da matafiya uku.

An kuma gano motar matafiya da aka ceto kirar Peugeot 307.

Gwamna Nasir El-Rufai ya nuna bacin ransa game da rahoton harin da aka kai kauyen Makoro Iri na karamar hukumar Kajuru, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka mutu, yayin da ya aika da ta’aziyya ga iyalansu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here