Gwamnati ta San Masu Daukar Nauyin Boko Haram: Hedikwatar Tsaro ta Musanta Neman Sojan da ya yi Furucin

 

Wani tsohon kwamandan rundunar sojan ruwa, Kunle Olawunmi, ya kasance cikin labarai bayan hirarsa ta kwanan nan a gidan talabijin na Channels.

Hedkwatar tsaro ta yi bayanin yanayin da ke tattare da gayyatar da ta yi wa tsohon jami’in sojan ruwan.

Gwamnatin tarayya ta sha shan suka daga ‘yan kasar kan karuwar rashin tsaro a fadin kasar.

FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta musanta rahotannin da ke cewa ta ayyana neman tsohon kwamandan rundunar sojan ruwa, Kunle Olawunmi, ruwa a jallo kan kalaman da ya yi yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya rawaito, Hedikwatar tsaro (DHQ) ta bayyana rahoton a matsayin mara tushe.

Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Benjamin Sawyerr, ya yi ikirarin cewa an gayyaci Olawunmi ne ta hanyar sakon tes don raba bayanan sirri da Sojojin.

DHQ ya ce:

‘Don Allah ‘yan jarida. Akwai labarai na jaridar Sahara reporters cewa DIA ta ba da umarnin a kama Cdre Olawunmi rtd. Wannan karya ne kuma ba gaskiya bane. Za mu ba da sanarwa nan ba da jimawa ba.”

Manjo Sawyerr ya bayyana cewa an gayyaci babban jami’in sojan ruwa mai ritaya ne kawai don ya zo ya raba bayanan da za su taimaka wa sojoji wajen yakar ‘yan tawaye da ‘yan fashi.

Mai magana da yawun DHQ ya bayar da hujjar cewa gayyatar ba ta zama izinin kamawa ba, Leadership ta rawaito.

Ya ce:

”Kungiyar leken asiri kamar dangi ne, wani daga DIA yana kallon babban jami’in yana magana kuma yanzu ya kira shi.‘Oga idan kana da irin wannan bayanin zai yi kyau ka raba wa DIA. Don Allah, za ka iya zuwa ranar Talata ka raba tare da mu domin ta taimaka wa hukumomin tsaro su magance matsalar a kan lokaci. ’Shin hakan ya zama izinin kamawa? Gayyata ba kamawa bane.”

Kunle Olawunmi ya yi ikirarin cewa ‘yan ta’addan Boko Haram sun taba ambaton sunayen wasu mutanen da ke aiki a wannan gwamnati a matsayin masu daukar nauyin ta’addanci.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here