Kuros Riba: ‘Yan Ta’adda Sun Kashe Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda
Wasu ‘yan ta’adda da ake zargin cewa ‘yan fashi da makami ne sun hallaka mataimakin kwamsihinan ‘yan sanda, Egbe Edum.
Edum, mai mukamin kwamishinan ‘yan sanda, ya gamu da ajalinsa a hanyarsa ta zuwa gida domin ganin iyalinsa.
‘Yan ta’adda sun kai farmaki kan Edum yayin da ya ke tafiya a gefen wata babbar hanya bayan motarsa ta lalace da tsakar dare.
Wasu miyagun ‘yan ta’adda, da har ya zuwa yanzu ba’a tantance su waye ba, sun kashe babban jami’in dan sanda a yankin kudu maso kudu.
Dan sandan, Egbe Edum, mai mukamin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, ya gamu da ajalinsa a kan hanyarsa ta zuwa ganin iyalinsa a jihar Kuros Riba.
Read Also:
‘Yan ta’addar sun kai wa Edum hari da safiyar ranar Laraba a yankin garin Calabar, babban birnin jihar Kuros Riba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kuros Riba, Irene Ugbo, ta tabbatarwa da jaridar Premium Times faruwar lamarin.
“Duk da har yanzu mu na kan gudanar da bincike, takaitaccen bayanin da ke hannunmu ya nuna cewa ya zo gari ne daga Maiduguri domin ziyarar iyalinsa.
Shi dan asalin nan ne. “Ya iso nan da misalin karfe 1:00 na dare, amma sai motarsa ta samu matsala a kan hanya, har ma ya Kira matarsa domin ta zo ta dauke shi.
“Ya na cikin tafiya da kafa a gefen hanya ne sai wasu miyagun batagari su ka far masa da sara da suka,” a cewar Ugbo.
Kakakin ta bayyana cewa ana zargin ‘yan fashi ne suka kai wa Edum hari.
Wata jaridar jihar Kuros Riba da ke wallafa labaranta a yanar gizo, CrossRiverWatch, ta wallafa labarin dauke da hoton motar Edum kaca-kaca da jini a gefen wata babbar hanya da ke Calabar.
Takardun motar sun tabbatar da cewa marigayi Edum ne ya mallake ta.