Jerin Jam’iyyu da ‘Yan Takarar Shugaban Kasa 8 da za su Gwabza a Zaben 2023

 

Manyan jam’iyyun siyasar Najeriya sun kammala zabukansu na fidda gwanin dan takarar shugaban kasa a zaben 2023.

APC, PDP, NNPP ADC, LP da dai sauran jam’iyyu duk sun fito da wadanda za su gwabza a zaben na 2023, inda kowace jam’iyya ke ci gaba shirin karbe kujerar Buhari a zaben.

Kowacce jam’iyya na bayyana kwarin gwiwar karbe kujerar ta Buhari, amma zabi dai ya rage wa ‘yan Najeriya su zabi wanda ya kwanta musu kuma suka amince da manufofinsa.

Batun manufofi, ‘yan siyasa da dama a jam’iyyu da dama sun sha bayyana tagomashin da suka tanadarwa ‘yan Najeriya, inda suke yawan lasa wa ‘yan kasar zuma a baki cewa suna hango gobe mai kyau.

Ko ya goben za ta kasance? Batu ne na sheke gobe ko kawo sauyi nagari, sai dai wanda ya shaida zaben na 2023.

A rahoton da muka hada, mun tattaro wasu daga cikin jam’iyyu masu tasiri a Najeriya da suka tsayar da ‘yan takara da kuma wadanda suka tsayar, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Jerin jam’iyyu da ‘yan takarar shugaban kasa na 2023

1. APC – Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

2. PDP – Alhaji Atiku Abubakar

3. NNPP – Eng. Rabiu Musa Kwankwaso

4. LP – Peter Obi

5. SDP – Prince Adewole Adebayo

6. ADC – Dumebi Kachikwu

7. YPP – Prince Malik Ado-Ibrahim

8. PRP – Kola Abiola

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here